KEDCO ta katse wa Jami’ar Dangote lantarki kan bashin miliyan N248

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya katse wutar lantarki ga Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, kan bashin Naira miliyan 248.

Manajin Darakta na KEDCO, Alhaji Abubakar Yusuf, ya shaida wa manema labarai a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Litinin da ta gabata cewa kamfanin ba shi da wani zaɓi illa ɗaukar mataki.

Ya ce, jami’ƙr ta biya Naira miliyan 20 ne kawai daga cikin Naira miliyan 248.

Yusuf ya sha alwashin cewa za a maido da wutar lantarki ne kawai idan hukumar ta yi “biya na mutunci”.

Ya kuma bayyana cewa KEDCO na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen wutar lantarki daga Kamfanin Dillancin Lantarki na Nijeriya (TCN), don haka akwai buƙatar a ruɓanya ƙokƙrin samar da kuɗaɗen shiga.

“Ina kira ga dukkan cibiyoyi da suka haɗa da na tarayya da na Jihohi da ma hukumomi da su daidaita basussukan da ke kan su.

“Muna da matakan da za mu tabbatar da karɓar kuɗaɗen da mu ke bi,” inji Yusuf.

By ukarofi