
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin raba wutar lantarki na jihar Kano, KEDCO ta sake haɗa wa Jami’ar kimiyya da fasaha ta Ɗangote da ke Wudil wutar lantarkinta bayan da aka biya Naira miliyan 100.
Mataimakin Shugaban makarantar (VC), Farfesa Musa Yakasai ya tabbatar da haka a wata hira ta waya da gidan ‘News Agency Nigeria’ a ranar juma’a inda ya ce KEDCO ta mayar da wutar ne da misalin ƙarfe 4 na yamma bayan da aka biya kuɗin.
KEDCO ta katse wutar ne bayan ikirarin cewa akwai bashin Naira miliyan 248 a kan jami’ar. Sannan, a watan, duk da an biya miliyan 20 cikin 60 da Jami’ar ke biya duk wata, sai da KEDCO ta katse wutar.
Kazalika, sai da gwamnatin jiha da asusun taimako na Ɗangote su ka bayar da gudummawa sannan aka biya miliyan ɗarin ga kamfanin.
Ɓangarorin biyu suna cigaba da ƙoƙari wajen warware bashin da aka gagara biya da kuma samar da hanyoyin rage ciyo su.
Daga bisani, hukumar makarantar ta yi godiya gare su, da kuma kira ga al’umma su kiyaye amfani da wutar lantarki ta hanyoyin da su ka dace.
