Ba mu ce Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ‘Yarjejeniyar Samoa’ ba – Majalisa ta yi amai ta lashe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar wakilai ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar haɗin gwiwa ta Samoa.

Kakakin majalisar, Akin Rotimi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Rotimi, wanda ke wakiltar mazaɓar Ikole/Oye, jihar Ekiti, ya ce saɓanin yadda kafafen yaɗa labarai suka riƙa yaɗawa, ‘yan majalisar sun yanke shawarar yin bincike a kan wasu batutuwan da ke cike da cece-kuce a cikin yarjejeniyar don tabbatar da cewa ba su saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara).

Ɗan majalisar na jam’iyyar All Progressiɓes Congress ya lura cewa majalisar ta buƙaci gwamnati da ta shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da yarjejeniyar.

Ya ce, “A yayin muhawarar, an nuna damuwa game da wasu sharuɗɗan da ake zargin suna tilasta tallafawa ‘yan Maɗigo, Luwaɗi, Auren Jinsi, da matsayin wani sharaɗi na kuɗi da sauran taimako daga ƙasashen da suka ci gaba.

“Bugu da ƙari, an bayyana fargaba game da wasu takamaiman kasidu da ke cikin yarjejeniyar, da suka haɗa da sashe na 2.5, 29.5, 36.2, da 88, waɗanda wasu ‘yan majalisar ke ganin ba za su yi daidai da muradun ƙasa da kimar Nijeriya ba, musamman ma idan babu wani sashe ta ya yi tanadin hakan.

“Ɗan Majalisar Wakilai Aliyu Sani Madaki ya bayar da hujjar cewa sashe na 97 na yarjejeniyar, wanda ya tabbatar da fifikon yarjejeniyar kan duk wata yarjejeniyoyin da ke cin karo da juna da suka shafi ƙasashen Tarayyar Turai ko Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, Caribbean, da Pacific, na iya tauyewa ‘yancin Nijeriya.

“A mayar da martani, shugaban majalisar, Julius Ihonɓbere (APC, Edo) ya bayyana cewa yarjejeniyar, kamar yadda aka gabatar a hukumance, ba ta haɗa da wasu tanade-tanade da suka shafi wani asusu na dala biliyan 150 ko kuma wasu sharuɗɗan da suka shafi ‘yancin LGBT a Nijeriya, saɓanin raɗe-raɗin jama’a.

“Da yake jaddada muhimmancin sa ido a majalisa, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda (PDP, Ribas) ya jaddada buƙatar yin gaskiya a tattaunawar yarjejeniya, inda ya yi misali da sashe na 12 na kundin tsarin mulkin Nijeriya (1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya tilasta wa majalisar shiga cikin irin waɗannan batutuwa. ”

Ya nace cewa majalisar ba ta yi kira da a dakatar da aiwatar da yarjejeniyar ba.

Ya ƙara da cewa, “Yana da kyau a fayyace cewa majalisar wakilai ba ta yanke shawarar dakatar da yarjejeniyar ba ko kuma a dakatar da aiwatar da ita, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cikin kuskure.

“Maimakon haka, majalisar ta yanke shawarar yin nazari sosai kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta Samoa ga duk wasu batutuwan da ke da alaƙa ta hanyar zaman majalisa.

“Bugu da ƙari, majalisar ta umarci kwamitocinta kan yarjejeniyoyin, ƙa’idoji da yarjejeniyoyin; Adalci; da Tsare-tsare na Ƙasa da Ci gaban Tattalin Arziki don yin hulɗa tare da masu ruwa da tsaki don magance duk wani shubuha a cikin yarjejeniyar. Ana sa ran kwamitocin za su miƙa rahotonsu ga majalisar cikin makonni huɗu.

“A yayin da take jaddada ƙudirinta na tsara manufofin Nijeriya na ƙetare daidai da muradun ƙasa, majalisar ta jaddada ƙudirinta na 7 (Tasiri da Jagorantar manufofin Nijeriya) don daidaita ƙa’idojin tsarin mulki tare da Dokar Amincewa da Yarjejeniya don daidaito da gaskiya.”

Yarjejeniyar Samoa, wacce aka rattaɓa hannu a ranar 15 ga Nuwamba, 2023, ta kafa sabon tsarin shari’a na dangantakar Tarayyar Turai da ƙasashe 79 na Afirka, Caribbean, da Pasifik, gami da 48 na Afirka, 16 Caribbean, da 15 na Pacific.

Wani rahoto na baya-bayan nan a wata jarida ta ƙasa (Daily Trust) ya yi zargin cewa yarjejeniyar Samoa ta haɗa da wani sashe da zai halasta maɗigo, luwaɗi, auren jinsi a Nijeriya, inda aka yi zargin cewa gwamnati ta karɓi wannan sharaɗin a matsayin wani rancen dala biliyan 150. 

Sai dai Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, da Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, sun musanta wannan iƙirarin yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.

By ukarofi