Jan da Els ma’aurata ne da suka kwashe kusan shekara 50 da aure. Sun mutu tare a farkon watan Yuni, da taimakon likitoci biyu da suka ba su maganin da ya taimaka masu suka mutu.
Jan da Els sun haɗu ne a makaranta a ajin rainon yara a lokacin suna ƙananan yara, sun kwashe tsawon rayuwasu suna soyayya. A lokacin Jan yana matashi yana bugawa ƙungiyar ƙwallon hockey ta ƙasar Netherlands wasa. Inda daga bisani ya zama kocin ƙungiyar. Els malamar makarantar firamare ce.
A ƙasar Netherlands, hakan ba laifi ba ne, ya halasta, sai dai hakan bai yi fice ba amman duk shekara ana samun ma’aurata da ke mutuwa ta wannan hanyar.
Kwana uku kafin su rasu bisa raɗin kansu, Jan da Els sun zauna a cikin rana a Friesland da ke Arewacin Netherlands. Ma’aurata ne da ke son tafiye-tafiye, kusan rayuwarsu a cikin motar ‘tafi da gidanka’ suke rayuwa ko kuma kwale-kwale.
Jan ɗan Shekara 70 na zaune kan sitiyarin motar tafi da gidanka, ya yi irin zaman da yake yi domin samun sauƙin ciwon bayan da ke damunsa. Matarsa Els tana da shekara 71 kuma tana da matsalar ƙwaƙwalwa, hakan ya sanya magana ke mata wahala.
A lokacin da suke matasa sun yi rayuwa ne a cikin jirgin ruwa mai tafi da gidanka. Daga bisani sun sayi jirgin ruwa na ɗaukar kaya domin yin kasuwancin jigilar kaya a cikin Netherlands.
Els ta haifi ɗansu guda wanda ta buƙaci a sakaya sunansa. Yana zama makaranta ne sai hutun ƙarshen mako yake komawa gida wajen iyayensa
Jan da Els na ƙirwirar tafiya mai dogon zango zuwa wurare masu ƙayatarwa.
A watan Nuwanba, 2022, a lokacin da gwaji ya tabbatar da tana da cutar mantuwar ta tafi ta bar mijinta da ɗanta a dakin duba marasa lafiya.
Jan ya ce, “Zan iya cewa matata ta yi fushi mai tsanani”.
A lokacin da Els ta fahimci cewa rashin lafiyarta da ta mijinta Jan babu sauƙi, sai suka fara tattaunawa da ɗansu kan mutuwa tare ta hanyar taimakon likitoci.
A ƙasar Netherlands, hakan ba laifi ba ne, a 2023, mutum 9,068 suka mutu ta hanyar taimakon likitoci, kashi biyar na mutanen da suka rasu.
“Da yawan likitoci ba sa son taimakawa mutane masu lalurar mantuwa wajen mutuwa” inji Dr Rosemarijn ɓan Bruchem ƙwararriya a asibitin Erasmus da ke Rotterdam.
A lokacin da likitan Jan da Els ya ƙi amincewa da buƙatarsu, sai suka tafi asibitin tafi da gidan da ke taimaka wa masu son su mutu cikin sauƙi. Kuma idan ma’aurata na son su mutu tare, dole sai ƙwararru sun tabbatar da cewa ba ɗaya ne yake tilasta wa ɗan uwansa ba.
Dr Bert Keizer ɗaya daga cikin likitocin da suka taimakawa masu so su mutu. Ya ce zai iya tunawa akwai lokacin da wasu ma’aurata suka je wajensa kuma ya fahimci lallai mijin ne ke tilastawa matar ɗaukar matakin, saboda haka sai ya yi ƙoƙarin tattauanwa da matar ita kaɗai, kuma nan ne ya fahimci mijin ne ke fama da rashin lafiya mai tsanani kuma shine ke son mutuwa amman banda ita.
Dr Keizer ya ce matar ta shaida masa cewa tana da wasu abubuwa da dama da take son cimmawa a rayuwa kuma bata shirya mutuwa ba.
Hakan ya ɗaya likitan bai aiwatar da hakan ba inda daga bisani mijin ya mutu sakamakon cutar da ke damunsa ita kuma matar har yanzu tana raye.A lokacin da likitan Jan da Els ya ƙi amincewa da buƙatarsu, sai suka tafi asibitin tafi da gidan dake taimakwa masu son su mutu cikin sauƙi. Kuma idan ma’aurata nason su mutu tare, dole sai ƙwararru sun tabbatar da cewa ba ɗaya ne yake tilastawa ɗan uwansa ba.
Kwana ɗaya kafin Jan da Els da su je wajen likitan da zai taimaka masu su mutu tare cikin sauƙi, sun zauna tare da ɗan su da jikokinsu. Jan ya yi ƙoƙarin yi wa ɗan nasu bayani kan motarsu ta tafi da gidanka da hanyar da zai bi wajen sayar da shi.
“Na yi tattaki tare da mahaifiyata zuwa bakin teku, yarana sun yi ta wasa da ita, ranar ta kasance mai tada hankali,” inji ɗan Jan da Els
“Zan iya tuna lokacin da muka ci abincin dare tare, na riƙa zubar da hawaye a lokacin da na kallesu a matsayin waɗanda muke zaune da su zama na ƙarshe tsakaninmu.”
A ranar Litinin da safe, manyan abokanansu sun hallara da ’yan uwansu da ɗan su da matarsa.
“Mun kwashe sa’o’i biyu kafin likita ya zo, mun tattauna kan yanayin rayuwarmu a baya, mun kuma saurari waƙoƙin da suke so tare.”
“Rabin sa’a ta ƙarshe da muka kasance tare da su ta kasance mafi muni, likitoci na zuwa komai ya faru cikin sauri, an yi duk abinda ya dace cikin ’yan mintoci komai ya ƙare,” inji ɗan Jan da Els
An yi wa Jan da Els allurai da magungunan da suka taimaka masu wajen mutuwa cikin sauƙi a ranar litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Har yanzu ba a sayar da motarsu mai tafi da gidanka. Ɗan Jan da Els ya yanke shawarar barin shi zuwa wani lokaci inda yake son zuwa hutu da matarsa da ’ya’yansa da motar.
“A ƙarshe dai dole zan sayar da ita amma kafin nan ina son in samu wani abu da za mu riƙa tuna wa ni da iyalaina kan motar.”
