An kama ɗan sanda da laifin fashi a bakin aiki

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da cafke sufeto Aminu Mohammed bisa zarginsa da hannu a wani fashi da makami a sashen ‘C’ da ke Lokoja babban birnin jihar. An kama shi ne a ranar Lahadi.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a SP William Aya, an kama sufeton ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar kan wasu gungun ‘yan fashi da makami da suka ƙware wajen satar kayan gida da motoci.

An gano motar da aka sace ne a wani taron bita da ke Ochadamu, kusa da Anyigba, inda wani ɗan sanda mai suna Arome Moses, ke ƙoƙarin canja launin motar.

Wasu da ke da masaniya kan mai motar ne suka gano motar da kuma lamarin fashin da ya faru a ranar 14 ga watan Yunin 2024. Sun sanar da hukuma, lamarin da ya kai ga kama sufeto tare da ƙwato motar da aka sace.

“Tuni an canja lambar motar zuwa lambar Abuja, kuma takardar dillalin mota, wanda aka dawo da shi a shekarar 2020, jami’in ya gabatar da shi a matsayin shaidar sayen ta. Wanda ya bugi motar ya sanya motar ta canja kala daga asalin kalarta karar,” inji SP Aya.

Bayan ƙarar ne aka kira ‘yan sanda daga sashin gaggawa da ke ofishin rundunar ‘yan sandan yankin, inda aka cafke wanda saci motar.

Ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar da ke cikin jerin sunayen ‘yan sanda da ake nema ruwa a jallo bisa wasu laifuka, ya amsa laifin satar tare da bayyana sunan ɗan sandan a matsayin wanda ya aikata laifin. Ya bayyana cewa an basu kwangilar yin fashin gidan mai motar ne musamman domin su samu motar da za a bai wa sufeton.

By ukarofi