An yaba wa Sardauna Solomon kan tsarin ɗibar ɗalibai a makarantar aikin jinya a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A halin yanzu iyayen yara da masu ruwa da tsaki da ma al’ummar jihar Nasarawa baki ɗaya suna ci gaba da yaba wa mahukuntar makarantar aikin jinya da unguwan zoma da ake kira School of Nursing and Midwifery a Turance na gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Mista Zari Sardauna Solomon dangane da tabbatar da adalci da kyakkyawarn tsari a yayin bai da gulbin karatu wa ɗalibai da suka caccanja musamman a shirin ɗaukar ɗalibai karatu a makarantar na bana shekarar 2024 da ake ciki.

Iyayen yaran da masu ruwa da tsaki musamman a fannin ilimin jihar sun yaba wa shugaban makarantar Mista Zari Sardauna Solomon ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a lokuta daban-daban don jin ra’ayin su game da yanayin tsarin ɗaukar ɗaliban karatu a makarantar na bana.

Sun ce ba shakka dole ne su yaba wa mahukuntar makarantar musamman shugabanta Mista Sardauna Solomon ɗin dangane da sabbin tsare-tsare da ya ƙirƙiro yake kuma aiwatar kawo yanzu a makarantar musamman wadanda suka shafi tsarin kwasan sabbin ɗaliban wɗdanda suka cancanta su  fara karatu a makarantar na bana 2024.

A cewar waɗanda aka zanta da sun shugaban makarantar ta aikin jinya da unguwar zoma mista Zari Sardauna Solomon tunda ya kama aiki a makarantar yana cigaba da yin ƙoƙari ne wajen tabbatar sai ɗalibai da suka cancanta suka kuma cika duka sharadun bai da damar karatu a makarantan ne kadai suke samun damar batare da yin la’akari da matsayin mutum ko ƙan siyasa ko wani abu makamancin haka ba.

Sun ce ba shakka kafin zuwan mista Sardauna Zari Solomon a matsayin shugaban makarantar an rika samun rashin adalci da magudi da kuma reshin bin tsari da uwa uba cin hanji a yayin bai da damar karatu wa sabbin daliban a makarantar inda saudayawa akan ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma sauran masu fada a ji cikin al’umma ne kawai ke iya turo ‘ya’yan su karatu a makarantar inda su kuma ‘ya’yan talakawa marasa galihu babu wanda ke kula dasu ko da ma sun cancanji a basu damar.

Sun kara da cewa a yanzu hakan yazame tarihi musamman idan akayi la’akari da abin da ya faru bana inda galibin wadanda suka samu damar fara karatun a makarantar ‘yan asalin jihar ne ‘ya’yan talakawa da suka kuma cika duka sharadun fara karatun na makarantar batare da an yi la’akari da rashin karfi ko matsayin iyayen su ba sabanin yadda lamarin yake a da.

Dangane da sauran nasarori da makarantar ta cimma kawo yanzu karkashin jagorancin shugaban ta Sardauna Solomon wadanda aka tattauna dasun duk sun kuma yaba masa inda suka shaida cewa tabbas a yanzu dalibai na samun cikakken ilimi da kwararrun malamai da sauran su ta sabbin tsare-tsaren inganta harkokin karatun a makarantar da mista Sardauna ke cigaba da kirkiro tareda aiwatarwa kawo yanzu.

A ƙarshe dai wakilinmu da ya kai ziyarar ta musamman makarantar dake babban hanyan Shendam a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar don bincikar yanayin tsarin bai da damar fara karatun na bana 2024 ya kuma gano cewa a halin yanzu dai an ma kammala shirin na kwasa ko bai da gulbin fara karatu a makarantar wato na zangon karatun da za za fara daga shekarar nan ta 2024 da ake ciki kenan yayin da sabbin daliban da suka yi nasarar samun damar sunma fara yin rajista don fara karatun su gadam-gadam.  

By ukarofi