Daga DAUDA USMAN a Legas
An bayyana cewar har yanzu dai Nijeriya tana cikin buƙatar ‘yan ƙasar su ci gaba da ƙoƙarin yi mata addu’o’in neman ƙarin zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.
Wani basarake a Legas, Alhaji Ibrahim Tanko Ɗan’iyan Legas ya bayyana hakan a Legas a lokacin da yake gabatar da saƙon sa na fatan alheri ga ‘yan Nijeriya tare da tayasu murna samun shigowar sabuwar shekarar Musulunci lami lafiya da kuma bayyana irin nasarorin da Nijeriyar ta samu a cikin waccan tsohuwar shekarar da kuma bayyana irin ƙalubalen da Nijeriyar ta fuskanta duk a cikin waccan tsohuwar shekarar da ta gabata a zantawarsa da Jaridar Bueprint Manhaja a Legas dangane da wannan al’amari.
Ɗan’iyan na Legas Alhaji Ibrahim Tanko ya ci gaba da bayyana wa Jaridar ta Manhaja cewa haƙiƙa a cikin tsohuwar shekarar da ta gabata Nijeriya ta samu nasarori daban-daban masu ya wa a ƙasar nan waɗanda suka haɗa da ƙarin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma samun sauƙin ta’addanci wanda ‘yan ta’adda suke yi a Arewacin Nijeriya da sauran makamantansu.
Haka kuma ya ce matsalolin da Nijeriyar ta fuskanta a tsohuwar shekarar da ta gabata sun haɗa da tsadar rayuwa al’umma da ƙarancin kuɗaɗe a hannuwan jama’a da sauran makamantansu. Ya ce akan haka yake ganin ya kamata ‘yan Nijeriya su ƙara ƙoƙari wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin neman amincewar Allah Ubangiji ya ƙarawa Nijeriya sassaucin waɗannan miyagun abubuwa baki ɗaya.
Haka kuma Ɗan’iyan na Legas ya ci gaba da jawo hankulan ‘yan Nijeriya musamman masu rajin gangamin kiran zanga-zanga a Nijeriya da su yi haƙuri su janye waɗannan buƙatun nasu domin al’ummar Nijeriya su samu natsuwa, a cewarsa domin zanga-zanga ba ita ce mafita ba.
Ya ce mafita ita ce a cigaba da yi wa shuwagabanni addu’o’i tare da ba su shawarwari masu inganci sai ka ga Allah ubangiji ya taimaka ya kawo wa ƙasar nan ƙarshen wannan al’amari Nijeriya ta dawo daidai da yadda ake buƙata tunda shuwagabannin suna iyakar ƙoƙarinsu su ga cewar sun kawo ƙarshen wannan al’amari.
Haka zalika ya cigaba da ta ya ‘yan uwa Musulmin Nijeriya da na sauran ƙasashen duniya baki ɗaya murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci, ya yi addu’ar cewar Allah Ubangiji ya ƙarawa Nijeriya nasarori ta dawo kamar sauran ƙasashen duniya waɗanda suka samu cigaba.
Sannan ya ci gaba da yin kira ga al’ummar Hausawa mazauna jihar Legas da na sauran jihohin Kudu da Yammacin Nijeriya da su ci gaba da zaman lafiya da sauran ƙabilu mazauna yankunan da suke zaune tare da su baki ɗaya.
