‘Yan bindiga sun kashe sarki da ɗansa a Taraba

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wasu ƴan bindiga a jihar Taraba sun kashe Sarkin Chanchanji, Mai girma Alhaji Tanimu Kunbiya da ɗansa, Yusuf Tanimu a lokacin da su ke dawowa daga ta’aziyya daga ƙaramar hukumar Takum a raɓar Juma’a.

Wata sanarwa daga ofishin mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai, Emmanuel Bello ta ce, gwamna Agbu Kefas ya samu labarin aukuwar lamarin tare da ta tausaya wa waɗanda ya shafa inda nan take ya bada umarnin gudanar da bincike domin gano makasan tare da alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.

Gwamnan ya jaddada cewa, za su cigaba da ɗaukar matakan bai wa jihar kariya daga ayyukan ɓarayi da satar mutane da makamantansu a dukkan sassanta.

Dakta Kefas, ya kuma jajentawa al’ummar Chanchanji da Takum inda ya yi kira gare su da su kwantar da hankali da kuma cigaba da taimaka wa zaman lafiya a yankunansu yayin da gwamnatinsa ke ƙoƙari wajen samar da tsaro ga kowa a jihar.

Wannan shi ne karo na uku cikin shekarar 2024 da ƴan bindiga ke kashe Sarki.

By Babaji