AIRLIN ta ƙuduri aniyar yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a Nasarawa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta ‘Advocacy for Integrity and Rule of Law Initiatiɓe’ (AIRLIN) ta ƙaddamar da reshen ta jihar Nasarawa mai mutane 20, wanda za su shiga yaƙi da wayar da kai game da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a tsakanin matasa, musamman a Arewacin Nijeriya.

Da yake jawabi a taron ranar Asabar a Lafiya, Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Ibrahim Muhammad Gamawa ya bayyana cewa su ƙungiyoyi ne da ba na siyasa ko addini ba, waɗanda ke da sha’awar ganin an magance matsalolin da ke kawo taɓarɓarewar tarbiyyar matasa a ƙasar nan.

Ya koka da yadda ake samun yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin al’ummar ƙasar nan.

Ya kuma ce, sace-sacen dukiyoyi da ake yi a faɗin ƙasar nan, matasa ne ke yi, ya kuma ƙalubalance su da su daina yin hakan kafin su lalata makomarsu.

Gamawa ya ƙara da cewa, ƙungiyar na haɗa kai da sauran ƙungiyoyi domin ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnati na magance munanan ɗabi’u da munanan laifuka a ƙasar nan.

Shugaban na ƙasa ya ci gaba da cewa,  ƙungiyar na fatan sabuwar Nijeriya da mutane za su mutunta ƙabila da addini.

Ya yi kira da a ƙara yawan ‘yan sa-kai da su shiga kamfen ɗin wayar da kan matasa waɗanda su ne makomar ƙasar nan.

Haka kuma, Alhaji Ibrahim Ibrahim, Kodinetan ƙungiyar na jihar Nasararawa ya bayyana cewa, kwamitin na da alhakin shirya taruka a ƙananan hukumomi a yankunansu domin wayar da matasa kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Kodinetan jihar ya ce, ‘yan kwamitin sun fito ne daga ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Josephine Malla daga ƙaramar hukumar Wamba da Bako Garba daga ƙaramar hukumar Toto waɗanda suka yi magana a madadin ’yan kwamitin sun bayyana cewa yawancin masu aikata laifuka suna yin abin da suke yi ne ta hanyar shan miyagun ƙwayoyi.

Don haka sun yi alƙawarin yin aiki da gaske a yankunansu don magance matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a jihar.

Ya bayyana cewa kwamitin zai taimaka wajen wayar da kan matasa musamman masu shaye-shaye a yankunansu kan aikata ayyukan da suka shafi ƙwaƙwalwa, lafiya, zamantakewa da tattalin arziki.

Ya kuma buƙaci matasa da su riƙa gudanar da ayyukansu cikin mutunci domin kada ’yan ta’adda da miyagun mutane su yi amfani da su wajen aikata laifuka.

By ukarofi