Ƙungiyar Middle Belt ta buƙaci Tinubu ya sauya shawarar kafa Ma’aikatar Kiwon Dabbobi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ƙungiyoyi da suka fito daga kudancin Nijeriya da waɗanda suka fito daga yankin tsakiyar Nijeriya, wato Middle Belt (MBF) ta buƙaci shugaba Bola Tinubu da ya janye shawarar kafa Ma’aikatar Kula da Dabbobi.

Ƙungiyar a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Dakta Pogu Bitrus ta kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya gaggauta rusa kwamitin shugaban ƙasa kan garambawul na kiwo.

Bitrus ya jaddada cewa samar da ma’aikatar kiwon dabbobi kaɗai ba tare da an fara magance matsalolin da suka shafi noma a Nijeriya ba tare da bayar da tallafi ga waɗanda bala’o’i ya rutsa da su a rikicin Fulani makiyaya da manoma, ba wai kawai rashin dubara ba ce, amma yana nuna kamar ba a damu da waɗanda abin ya shafa ba ne.

Ya ce, “Ƙungiyar Middle Belt ta bayyana cewa a cikin sanarwar manufofin kafa sabuwar ma’aikatar ita ce ma’aikatar za ta magance abubuwan da gwamnati ta bata a matsayin “rikicin manoma da makiyaya”, amma wanda a zahiri shi ne ajanda ta kwace ƙasa ta hanyar. ’Yan ta’addar Fulani masu ɗauke da makamai na neman mayar da Nijeriya wani yanki na tsanar Fulani daga yankin yammacin Afirka da Afirka ta Tsakiya.

“Fulani na ci gaba da tabbatar da cewa Nijeriya ita ce gadon da Allah ya ba su, kuma sun yi ikirarin cewa ƙa’idojin ECOWAS kan canja yanayi da dokokinta sun bai wa Fulani daga ko ina a yammacin Afirka damar shiga ba tare da wani sharaɗi ba su zauna a Nijeriya. Wannan shiri na kwace filayen Fulani shi ne ya yi sanadin mutuwar dubban ’yan Nijeriya, tare da raba miliyoyin ‘yan Nijeriya da muhallansu tare da mayar da su ‘yan gudun hijira a cikin ƙasarsu, ba su iya komawa garim kakanninsu da wasunsu a wasu ƙasashe kamar su; Kamaru, a matsayin ‘yan gudun hijira.

“Ba mu yarda cewa masu goyon bayan sabuwar ma’aikatar suna da kishin ƙasa a zuciya ba, suna wakiltar mugayen muradu na musamman. Suna so su ƙara tunzura waɗanda aka riga aka tunzurar. Hankalinsu shi ne kwace filaye da karkatar da albarkatun da ke da alaƙa da siyasa. Wannan shiri na kwace filayen Fulani shi ne ke haddasa ɗimbin ƙarancin abinci, sannan kuma ya haifar wa al’ummar ƙasar yanayi na rashin tsaro a Nijeriya wanda ya sa ake shigo da abinci da yawa saboda manoma a yankin ba sa iya shiga gonakinsu. Don haka a samar da ma’aikatar kiwon dabbobi kawai ba tare da an fara magance matsalolin da suka shafi noma a Nijeriya ba tare da bayar da tallafi ga waɗanda bala’in ya rutsa da su a rikicin Fulani makiyaya da manoma, ba wai kawai rashin dabara ba ce, amma nuna halin ko in kula ne ga waɗanda abin ya shafa.

By ukarofi