Ba zan yi shiru kan tashin hankalin da al’ummar Gaza ke ciki ba – Kamala Harris

Spread the love

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, da jam’iyyar Democrats ke gaf da tabbatar da ita a matsayin ‘yar takararta a zaɓen ƙasar da ke tafe, ta ce ba zata yi shiru kan tashin hankalin da al’ummar Gaza ke ciki ba.

Harris ta sha wannan alwashi ne yayin taron manama labarai da ta kira a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan ganawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ke ziyara a birnin Washington.

Kalaman mataimakiyar shugaban na Amurka dai alama ce da ke nuna wani muhimmin sauyi da ake shirin samu dangane da manufofin ƙasar a yaƙin Gaza.

A yayin da shugaba mai barin gado Joe Biden ke cigaba da ƙoƙarin ririta ɗorewar kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da Firaministan Isra’ila, ga dukkanin alamu lamurra za su sauya zuwa nan gaba, la’akari da yadda Kamala Harris ta fito fili wajen matsin lamba gareshi kan buƙatar gaggauta kawo ƙarshen mummunan yanayin da Falasɗinawa ke ciki ta hanyar amincewa da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin da aka shafe sama da watanni bakwai ana yi a Gaza.

Harris ta kuma nanata buƙatar samar da Ƙasar Falasɗinu, ɗaya daga cikin hanyoyin da aka daɗe da zaɓa domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A dai ranar ta Alhamis Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Joe Biden a karin farko, tun bayan haɗuwar da suka yi a birnin Tel Aɓiɓe, sa’o’i bayan farmakin da mayakan Hamas suka kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

By ukarofi