Ƙungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da kisan masu zanga-zanga 13 a faɗin Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar Isa Sanusi ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya na mai umartar gwamnatin Nijeriya ta gudanar da bincike domin gurfanar da waɗanda suk aikata wannan laifin.
Ƙungiyar ta ce, waɗanda aka kashe sun fito daga sashe daban daban na ƙasar nan, mutum shida a Suleja da ke Jihar Neja, huɗu a Maiduguri da kuma mutum uku a Kaduna.
Ƙungiyar ta cigaba da cewa, binciken su, ya nuna cewa jami’an tsaro a wannan wurare sun buɗe ma masu zanga-zanga wuta lokacinnda suke nuna rashin jin daɗinsu game da tsadar rayuwa.
Amma rundunar ‘yan sandan Jihar Neja sun musanta wannan zargin, sun ce ba wanda ya rasa ran shi sai dai wanda suka samu rauni, suma an kai su asibiti domin amsar magani da kulawa.
