
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani abin tausayi a jihar Katsina ya auku yayin da jami’an Ƴan sanda su ka harbe abokin aikinsu bisa kuskure a lokacin da su ke ƙoƙarin tarwatsa an zanga-zanga.
Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a inda shaidu su ka bayyana cewa ana gudanar da zanga-zangar cikin lumana kafin jami’ai su shiga cikin inda bayan haka ne aka samu hargitsi sakamakon harbe-harbe da ƴan sandan su ka fara yi.
Sakamakon ƙunci da al’umma a jihar ke ciki sanadiyyar tsadar rayuwa da rashin tsaro, ya sa mutane su ka yi dandazo don nuna damuwarsu game da halin da su ka tsinci kansu a yankin.
Kisan ɗan sandan ya haifar da cecekuce a cikin al’umma inda wasu ke ganin illar amfani da ƙarfi daga hukumar da ke kula da gudanar zanga-zanga.
Kawo yanzu dai babu wani jawabi daga rundunar ‘Yan sanda game da lamarin, amma kuma hakan ya sa ake zaman ɗar-ɗar tsakanin al’umma da kuma jami’an ‘Yan sanda.
Za a cigaba da gudanar da zanga-zangar yayin da ake ƙara nuna damuwa game da halin da al’umma ke ciki a faɗin Nijeriya.
