Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kashe Naira Miliyan 596 wajen samar da kayayyakin ofis da sauran ababen more rayuwa a ma’aikatun gwamnatin jihar a cikin zangon farko da na biyu na kasafin kuɗin shekarar 2024.
Baya ga haka, gwamnati ta ba da umarnin sake sabunta kashi na biyu na ayyukan kasafin kuɗin jihar nan take.
Da yake mayar da martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa kan yadda kasafin kuɗin jihar ke gudana, inda aka tanadi zunzurutun kuɗi Naira biliyan 10 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kashe kan kayayyakin ofis, mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya buƙaci jama’a da su yi watsi da wannan adadi, wanda a cewarsa an yi shi ne don yi wa gwamnati ƙarafi.
A cewar Dawakin-Tofa, gwamnatin Gwamna Yusuf ta ba da fifiko sosai kan gaskiyar kasafin kuɗi domin a samu gaskiya da riƙon amana a harkokin mulki.
