Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A wani ƙazamin hari da wasu ’yan bindiga suka kai ƙauyen Karfen Sarki da ke ƙaramar Hukumar Gudu a Jihar Sakkwato, sun kashe mutane bakwai ciki har da jami’an sabuwar rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta kafa su biyar.
Shugaban ƙaramar hukumar Gudu, Hon. Umar Maikano Balle, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata.
A cewar Balle, ’yan bindigar sun yi wa mutanen kwanton ɓauna, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.
“Kwarai jami’an sabuwar rundunar tsaron yankin suna ƙoƙarin daƙile hare-haren ’yan bindiga na lokaci-lokaci har ya zuwa yanzu, wanda hakan ya yi sanadin rasa mambobinsu biyar,” inji Balle.
Wannan dai ba shi ne karon farko da yankin ya fuskanci irin wannan tashin hankali ba. A shekarar 2019, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Hakimin Balle, Alhaji Ibrahim Aliyu, bayan wata taƙaddama da ta haɗa da ɗan uwansa da kuma waɗanda ake zargin.
An yi jana’izar mutane bakwai da wannan sabon harin ya rutsa da su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
ƙaramar hukumar Gudu dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar Sokoto 13 da ke fama da matsalar ’yan fashin daji. Yankin da ke da kusanci da Jamhuriyar Nijar ya sanya ya zama wuri na satar shanu da hare-haren wuce gona da iri.
A shekarar 2020, yankin ya yi ƙaurin suna a lokacin da jagoran ‘yan jihadi na Mali Lakuruje ya karɓe iko, ya sanya haraji tare da aiwatar da tsarin shari’a a yankunan karkara. Ya ɗauki wani yunƙuri na haɗin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda, da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin fatattakar ƙungiyar Lakuruje daga dazukan Gudu.
Rahotanni daga wancan lokacin sun nuna cewa tun farko al’ummomin Fulani ne suka gayyace su domin neman kariya daga ƙaruwar satar shanu da ‘yan fashi. Bayan sun fatattaki ‘yan ta’addan, ‘yan jihadi sun kafa nasu mulkin, inda suka mayar da yankin ya zama na su.
Tsohuwar gwamnatin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta kashe sama da naira biliyan 1.7 domin gina makarantar sakandare ta kwana a garin Balle hedikwatar ƙaramar hukumar Gudu.
Duk da haka, saboda rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, an watsi da makarantar.
Gudu ita ce ƙaramar hukuma ɗaya tilo a cikin 774 a Nijeriya da har yanzu ba ta da makarantar sakandare ta kwana.
