Yunwa ce ta saka ni satar doya, inji wani mutum a kotu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani mutum mara aikin yi mai suna Cletus Gandu mai shekaru 40, a ranar Laraba ya bayyana cewa ya saci doya guda biyu ne saboda yana jin yunwa.

Hukumar NSCDC, ta tuhumi Gandu da aikata laifuka da kuma sata.

Gandu ya shaida wa Kotun Majistare da ke Kafanchan, Jihar Kaduna cewa, “Yunwa ta sa na saci doya sau biyu, inda ya roƙi afuwar kotu.”

Alƙalin kotun, Michael Bawa, ya ɗage yanke hukunci har zuwa ranar 6 ga watan Agusta, bayan da wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa.

Bawa ya bayar da umarnin a tsare shi.

Tun da farko, ɗan sanda mai shigar da aara na NSCDC, Marcus Audu ya shaida wa kotun cewa mai shigar da ƙara, Alice Daniel ta kai rahoton lamarin a ofishin hukumar da ke Kafanchan a ranar 15 ga watan Yuli.

Audu ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya saci doyan ne a gonar mai ƙara da ke Zonkwa sau biyu.

Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 327 da 270 na dokar laifuka ta jihar Kaduna.

By ukarofi