
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake cigaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a yau Litinin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da shugabannin harkar tsaro a Fadar shugaban ƙasa.
Su na gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Majalisar tsaro ta Ƙasa inda ake tattauna batun zanga-zangar tsadar rayuwa da gazawar shugabanci.
Mahlarta taron sun haɗa da; Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima; Shugaban Ma’aikatan tsaro, Janar Christopher Musa; Shugaban Ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; Sufeto Janar na Ƴan sanda, Kayode Egbetokun da sauran manyan ma’aikatan harkar tsaro.
A jiya ne shugaba Tinubu yi gabatar da jawabi game da halin da ƙasa ke ciki inda ya nemi ƴan zanga-zangar su dakatar da ita tare da neman tattaunawa.
A halin yanzu dai ana cigaba da gudanar da zanga-zangar a faɗin Nijeriya.
