
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
‘Yan sandan farin kaya ta DSS ta sanar da kama wasu teloli a jihar Kano da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha waɗanda ake zargin masu zanga-zangar tsadar rayuwa ne za su yi amfani da su.
Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunaya ya faɗi hakan a ranar Litinin cikin wata takarda da ya fitar, ya na mai cewa su na binciken gano waɗanda ke ɗaukar nauyi tare da kama su don a hukunta su.
Haka nan, Peter ya ce rahoton da ke yawo cewa sun kama wani mai suna Adaramoye Michael, shugaban ƙungiyar ‘youth rights campaign’ da aka fi sani da suna Michael Lenin ba gaskiya ba ne, ya na mai cewa DSS ta ce ɗan gwagwarmayar ba ya hannunta.
A wani labarin, hukumar ƴan sanda ta ruwaito cewa ta kama wani mai raba tutocin Rasha tare da masu zanga-zanga guda 30 a ranar Litinin.
Ƙasar Rasha dai ta kasance ta na da alaƙar siyasa da ke tasiri a ƙasashen yammacin Afirka wanda hakan ya haifar da canjin wasu gwamnatoci ba bisa doka ba a ƙasashe kamar su Nijar, Mali da Burkina Faso.
Kazalika, ofishin jakadancin Rasha da ke Nijeriya ya musanta hannu a cikin yaɗa tutocin inda ya ce hakan mai yiwuwa raɗin kai ne ga masu zanga-zangar wanda bai shafi wani tsari na gwamnatin Rasha ko wata matsaya ba kan hakan.
