
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin sayar da buhun shinkafa mai nauyin 50kg kan Naira 40,000 ga al’umma da nufin rage raɗaɗin matsalar samun abinci a Nijeriya.
Wata takarda daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin da su ka shafi gwamnati da ke ɗauke da sa hannun Daraktan albarkatun al’umma na ma’aikatar, Jaiyesimi Abimbola ta ce duk ma’aikata da ke muradin sayar shinkafar a kan farashin, akwai bayanai da za su cike ta yanar gizo ga ofishin Daraktan wanda hakan zai bada damar mallakar sa.
Sannan, za a wakilta masu lura da biyan kuɗin shinkafar da raba ta ga mutanen, da kuma tabbatar da yin adalci daga majalisar haɗaka ta ma’aikatar.
Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Muhammed ya ce, wannan huɓɓasa ɗaya ne daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen ganin an samar da sauƙin rayuwa wa al’ummar Nijeriya.
