Shugaban kamfanin NNPC Mele kyari yace kamfani bai karya doka ba wajen mu’amalar su da abokan kasuwanci, don haka a daina zargin kamfanin da kokarin kawo cikas ga harkar mai a ƙasar
Kyari, yayi wannan jawabi ne a yayin da gurfana a gaban kwamitin majalisa domin amsa tambayoyi a kan wasu batutuwa da suka taso. Inda ya bayyana kasuwanci tatar mai, kasuwanci ne da kowa zai iya shigar sa saboda babu shubuha a cikin sa.
Ya cigaba da cewa, dokar a bayyane take a kan harkokin ɗanyen mai da kuma sayarwa matatun mai na gida. Sannan yace dokar, ta bayyana dole a samu mai kaya da kuma mai saya kafin ƙulla wani kasuwanci.
A kan batun shigo da gurɓataccen mai a ƙasar, yace ba hurumin kamfanin NNPC bane, akwai hukumomin na gwamnati da wannan ne hurumin su.
Kyari ya yaba da kwamitin majalisar bisa batun haska tattaunawar kai tsaye domin ƴan ƙasa su gani kuma su ji abinda ke wakana .
Daga ƙarshe ya bayyana a shirye kamfanin yake ya ba kwamitin haɗin kai domin samun maslaha. ” mu na da biyayya da sanin yakamata a duk wani abu da ya shafi cigaban ƙasa.
