Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa ya raba wa al’ummomin da iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafa a ƙananan hukumomin Argungu, Augie, Suru da Bagudo.
Alhaji Adamu Yusuf Gulma (Danmadamin Kabi) shi ne ya jagoranci tawagar a madadin Sanatan a waɗannan yankunan.
Da ya ke jawabi a garin Tiggi ya bayyana cewa Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi yana sane da irin damuwar da suka shiga kuma yana mai jajenta musu tare da fatar Allah ya mayar musu da alheri jikan waɗanda suka rasu.
Ya ƙara da cewa a matsayin su na Musulmi su mayar da lamarin ga Allah kuma su ɗauki abin a matsayin jarabawa.
Sanatan ya bai wa garuruwan Tiggi, Bayawa da Kamfani da Kwakware da dai sauransu kowane naira dubu dari biyar-biyar da buhu hamsin-hamsin na abinci.
Ya kuma bayar da tabbacin kai koke tare da bibiyar a wajen hukumar da abin ya shafa har sai sun samu irin tallafin da ya kamata in Sha Allahu.
Wata mai kama da wannan shi ma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar ƙananan hukumomin Argungu da Augie Honarabul Sani Yakub Noma ya bayar da tallafin buhunan abinci kayan kwanciya da kuɗaɗe ga waɗanda iftila’in ya shafa tare da fatar Allah ya kawo musu sauƙi.
