
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar gudanar da jarrabawar ƙarshe ta ƴan makarantun sekandire a yammacin Afirka, WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi na shaidar kammala sekandire a Afirka ta yamma (WASSCE).
An samu sanarwar ne a lokacin da ofishinta ya wallafa bayanin a kafarta ta X.
Ta ce, ta na ya mai sanar da ɗaliban da suka rubuta jarrabawar cewa a yau 12 ga watan Agusta, 2024 ta sako sakamakon na shekarar inda ta bayar da adireshi kamar haka ga waɗanda ke son duba nasu; http://waecdirect.org.
