
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fara ziyarar musamman ta tsawon kwanaki uku a ƙasar Equatorial Guinea.
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Tinubu zai bar Abuja ne a ranar Talata zuwa Malabo, babban birnin ƙasar inda zai gana da shugaban ƙasar, Nguema Mbasogo a Fadar shugaban ƙasa da ke birnin.
A lokacin ziyarar, Tinubu zai tattauna da takwaran nasa kan inganta ababen da ƙasashen biyu suka haɗu a kai ciki har da matsalolin tsaro, mai da kuma gas.
Ƴan rakiyar shugaba Tinubu sune; Ministan harkokin ƙasashen waje, Jakada Yusuf Tuggar da wasu mambobin gwamnatinsa waɗanda zasu shiga cikin ƙulla yarjejeniya kan abubuwa da ke tsakanin Nijeriya da Equatorial Guinea da kuma karfafa alaƙa a tsakanin su.
A watan Maris, 2023 ne Tinubu ya karɓi baƙoncin wakilan Shugaba Nguema a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda suka tattauna batutuwan tsaro wanda Nijeriya ta tabbatar da ƙoƙarinta na inganta harkar tsaro na kan gaɓar tekun Gulf na ƙasar Guinea.
