
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ɓukaci ƴan Nijeriya su daina kanbama gidan shugaba Bola Ahmed Tinubu na jihar Legas inda ya ce nasa da ke Maiduguri a jihar Borno ya fi wannan ƙawatuwa.
Shettima ya faɗi haka ne a lokacin taron ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Navigating the Politics of Universal Education Policies in Nigeria’ da Farfesa Modupe Adelabu daga Jami’ar Obafemi Awolowo ya wallafa, wanda aka gudanar a Abuja.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, nan ba da jimawa ba za su fara ganin amfanin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka wajen daidaita al’amura a Nijeriya.
Haka kuma, ya ce kamata ya yi a ce ƴan Nijeriya su mayar da hankula waje samar da mafita ga muhimman ababen da su ka dame su, ba akan halin tsanani da ƙasar ta tsinci kanta ba a baya da kuma yanzu.
Ya ce, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu mutum ne da ya kamata mu bai wa yardarmu mu kuma amince masa. Ba ina yaudarar siyasa ba ne. Ina magana ne har cikin zuciyata. Na ga manufar Bola Tinubu, kuma ya na da manufa mai kyau.”
Ya ƙara da cewa, tattalin arziƙin Nijeriya ya ɗakko hanyar bunƙasa yayin da gwamnati ke cigaba da bin hanyoyin da suka dace wajen ganin an cimma hakan a faɗin ƙasar baki ɗaya, ya na mai bada misali da adadin gangar mai da Nijeriya ke shigowa da ita a rana wanda a yanzu ya kai miliyan 1.7 sannan kuma darajar Naira na farfaɗowa.
