Minista ya gana da masu ruwa da tsaki kan cinikin ɗanyen mai a Naira

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya gana da manyan masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas, biyo bayan umarnin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar na kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), na sayar da ɗanyen mai ga matatun man ƙasar a naira.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, Babban Daraktan Rukunin na NNPC, Mele Kyari, Shugaban Hukumar Kula da Harajin Harakokin Cikin Gida ta Tarayya, Dokta Zacch Adedeji, da Sakatariyar na dindindin na Ma’aikatar Kuci, Lydia Jafiya.

Ma’aikatar kuɗi ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na ɗ, ta ce an gudanar da taron ne a ranar Litinin a Abuja.

Ya bayyana cewa, an yi shirin ne don ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida da kuma tallafa wa ayyukan ci gaba da ayyukan matatun na cikin gida ciki har da matatar Dangote.

“A ranar Litinin, Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya jagoranci wani muhimmin taro da nufin aiwatar da umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar na Kamfanin Mai na Nijeriya Limited na sayar da ɗanyen mai ga matatun man ƙasar a cikin Naira,” inji sanarwar.

By ukarofi