Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kantoman riƙo na ƙaramar Hukumar Gaya ya raba takardar ɗaukar aiki na wucin-gadi ga matasan yankin a fannin ilimi da lafiya.
Ya ce bai wa matasan aikin wucin-gadin tausaya wa matasa ne domin ba su aikin yi kuma hakan koyi ne da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda a baya ya bai wa ‘yan Besda 150 takardar aiki na dindindin.
Ya ce yanzu sun haɗa da mutum 74 da aka baiwa takardar aiki na wucin gadin domin a cikinsu akwai wanda ya shekara 12 yana aikin amma an shekaru takwas ko kwandala ba a ba su wannan tasa suka tausaya musu suka ga dacewar ba su aikin wucin-gadi kafin lokaci ya yi da za a mayar da su na dindindin.
Hon. Abubakar Jazuli Usman Gaya ya ce sun ɗauki ma’aikatan ran 1 ga watan Augusta kuma al’adar Gwamnatin Jihar Kano duk ran 25 ma’aikaci zai ji albashinsa saboda haka sun sa musu alawus ɗinsu na watan da za su riƙa basu duk wata.
Ya ce shi aiki yana da ƙa’ida saboda haka sun saka mutane da za su riƙa kula dasu su tabbatar kowanne na zuwa aiki duk da cewa sun san mutane ne jajirtattu kuma yan kwankwasiyya ne na asali ko an busu ko ba a busu ba zasu ce wajen aiki.
Hon. Abubakar Jazuli Usman Gaya ya ce kwamitin tantance ma’aikata ya bai wa ɗan kowane jam’iyya aiki ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba wannan kuwa ko kana jam’iyyar NNPP ko baka yi tarbiyya ce ta Gwamnan Jihar Kano da ita kuma suke koyi.
Gaya ya yi kira ga al’ummar yankin su cigaba da bai wa gwamnatin Jihar Kano da na ƙaramar hukumar haɗin kai don cimma burinta na bunƙasa ci gaban al’umma.
