Manoman Kogi sun buƙaci a yi addu’ar samun ruwan sama

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Manoman Jihar Kogi ta yi kira da a yi addu’o’in samun ruwan sama, sakamakon mummunan kamfar ruwan da ake yi a gonaki da kuma ƙarancin abinci a jihar.

Kwamishinan aikin gona Mr Timothy Ojomah da shugaban ƙungiyar manoma, AFAN, na jihar, Salihu Adobayi, su ne suka yi kiran a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN, a Lakwaja.

Suka ce tsawon sama da wata ɗaya yanzu babu ruwan sama, ƙila illar rashinsa za ta shafi tallafin da gwamnati ta bai wa manoma don bunƙasa samar da abinci a jihar.

Shugaban ƙungiyar manoman ya ce, kafin a shiga wannan yanayin na rashin ruwan, yanayin damunar ya ƙarfafa wa manoma gwiwa a jihar.

“Abin takaici yanzu abin da muke fuskanta a faɗin jihar shi ne rashin ruwa. Rashin ya shafi dukkanin abubuwan da aka shuka, musamman ma shinkafa fa masara” inji shugaban. 

“Abin takaici, muna fuskantar fari a faɗin jihar a halin yanzu. Ya shafi yawancin amfanin gonakin mu. Mafi yawan abin ya shafa sun haɗa da noman shinkafa da masara, musamman waɗanda suka kusa isa girbi. Na kasance a gonar masara jiya, kuma abin takaici ne,” inji Adobayi.

A cewar Adobayi, kafin fari, abin da aka samu a galibin gonaki a fadin jihar yana da matuƙar kwarin gwiwa.

“Wannan ya faru ne saboda gwamnati ta samar da fili sama da hekta 8,000 ga manoma daban-daban domin noman Shinkafa, Masara da Rogo, kuma duk an noma su kuma sun yi kyau sosai har sai da fari ya shigo.

“Fatan mu ga Allah ne da hasashen NiMET cewa za a iya samun ruwan sama mai tsanani daga ranar 18 ga Agusta.

“Idan ruwan sama ya sauka, akwai fatan za a iya ceton wasu amfanin gona. Amma idan har ta ci gaba, to ba za ta yi mana kyau ba domin amfanin gona ya dogara da ruwa don tsira,” inji shi.

Ojomah ya bayyana cewa gwamnatin jihar na duba damarar shiga cikakken aikin noma ta hanyar samar da kayayyakin ban ruwa, musamman famfunan ruwa masu amfani da hasken rana ga manoma.

“Muna tunanin hanyar da za a bi domin wannan burbushin mai ba shi da arha don saya, kuma yana karuwa da girma kowace rana.

By ukarofi