Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar Masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Ɗan-Yaya.
A wata sanarwa da ta fito daga Fadar gwamnati, Shugaban ya bayyana marigayin sarkin a matsayin hazikin shugaba da ya yi amfani da muƙaminsa wajen yi wa al’umma hidima.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan sarkin, Ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar Masarautar da ma Najeriya haƙurin rashin sa.
Marigayi sarkin Ningi ya rasu ne a yau ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, 2024.

