Ku ƙaurace wa wuraren ambaliya – Gwamnatin Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMAMD

Biyo bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje sama da 200 a ƙananan hukumomin Sabon Gari da Zariya a ranar Litinin, Gwamnatin Jihar Kaduna ta buƙaci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su gaggauta ficewa.

Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KASEMA) Dakta Usman Hayatu-Mazadu wanda ya yi wannan roƙo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Talata, inda ya yi bayani dalla-dalla kan ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na daƙile illar ambaliyar.

Waɗannan ƙoƙarin sun haɗa da tsaftace magudanun ruwa da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a.

Duk da waɗannan matakan, Mazadu ya bayyana cewa wasu mazauna garin sun yi watsi da gargaɗin da aka yi na ficewa, wanda ya janyo hasarar dukiya mai yawa.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kan mazauna wurin domin kare lafiyarsu, ya kuma shawarci manoma da su koma garuruwan da gwamnatin jihar ta ba da madadin filayen.

Mazadu ya bayyana cewa, “Ambaliyar da ta afku a baya-bayan nan ta yi ɓarna sosai, inda sama da gidaje 200 suka lalace. Mun ɗauki matakan da suka dace bisa hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi, ciki har da kawar da tsofaffin magudanan ruwa, wanda hakan ya taimaka wajen rage illar ambaliyar a wasu yankunan.”

Mazadu ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi wani nauyi ne na haɗin gwiwa, inda ya buƙaci mazauna yankin da su yi biyayya ga shawarwarin tsaro da kuma kaura daga wurare masu haɗari.

By ukarofi