Ƙungiyoyi 60 da ke fafutukar kare ƴancin ƴan jarida a sassan duniya, sun ratabba hannu kan wata wasiƙasa da ke neman ƙungiyar Tarayyar Turai ta katse yarjejeniyar taimakekeniya da ke tsakaninta da Isra’ila, lura da yadda ƙasar ke cin zarafi da kuma kisan ƴan jarida a yanzkin Gaza.
A cikin wannan wasiƙa, ƙungiyoyin sun ce ta hanyar dakatar da wannan yarjejeniya, Tarayyar Turai za ta iya ɗaukar matakan sanya takunkumai a kan manyan jami’an gwamnatin Isra’ila da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen tauye haƙƙi da kuma kisan ma’aikatan yaɗa labarai musamman a yakin Gaza da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan.
An tura wannan wasiƙar ce zuwa ga shugaban ofishin kare manufofin ƙetare na ƙungiyar EU Joseph Borrell da kuma mataimakinsa Caldis Dombroɓskis, tare da jaddada fatan ganin cewa ƙungiyar ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen kisan da ake yi wa ƴan jarida a yankin Falasɗinu.
Alƙaluma da ƙungiyoyin kare haƙƙin ‘yan jaridu a duniya suka fitar, na nuni da cewa adadin ma’aikatan yaɗa labarai da suka rasa rayukansu daga ranar 7 ga watan oktoba lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Hamas ya ɓarke, sun kai 130 yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ƙungiyoyin sun gabatar da wannan wasiƙa ce a daidai lokacin da ministocin harkokin waje na ƙungiyar ta Turai ke shirin gudanar da taro ranar 29 ga wannan wata na Agusta a birnin Brussels. Wasu daga cikin ƙungiyoyin da suka rattaba hannu kan wasiƙar har da Reporters Sans Frontiers, FPU da kuma HRW.
