Cire tallafin mai: Har yanzu gwamnati ba ta fara ba mu tallafin N25,000 da ta yi alƙawari ba — ‘Yan fansho

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mambobin ƙungiyar ‘Yan Fansho ta ƙasa a ranar Talata sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta cika alƙawarin da ta yi na biyansu Naira 25,000 na wata-wata domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

Tsoffin ma’aikatan sun kuma nemi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya bada umarni ga hukumar kula da albashi ta ƙasa da ta fitar da sanarwar bada damar aiwatar da mafi ƙanƙantar kuɗin fansho kamar yadda aka amince da mafi ƙarancin albashi.

A shekarar da ta gabata ne dai, gwamnatin ta yi alƙawarin biyan ma’aikata dubu 35 da ‘yan fasho Naira 25,000 na tsawon watanni 6 a matsayin tallafin rage raɗaɗi.

Sai dai binciken Daily Trust ya gano cewa, ba a biya ‘yan fanshon koda na wata ɗaya ba.

Da ya ke zantawa da Daily Trust a Abuja, mai magana da yawun ƙungiyar ‘yan fanshon, Bunmi Ogunkolade ya yi bayanin cewa, ƙungiyar ta miƙa kokenta ta hanyoyin da su ka dace amma har yanzu ba a saurari koken nasu ba.

“Mun rubuta wasiƙoƙi da dama zuwa ga ma’aikatar jinƙai da yaƙi da talauci. Mun kai ziyara da dama zuwa ma’aikatar. Amma an faɗa mana cewa batun mu an jingine shi saboda abinda ya faru a ma’aikatar.”

Sannan ya ce sun kai ƙorafinsu zuwa majalisar wakilai, amma har yanzu ba a dube su ba.

By ukarofi