2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja, inji PDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya na tattaunawa kan yuwuwar haɗaka domin goyon bayan ɗan takara don fafatawa da jam’iyyar APC da fitar da ‘yan Nijeriya daga yunwa da taɓarɓarewar tsaro gabanin zaɓen Shugaban ƙasa na 2027, in ji kakakin jam’iyyar PDP a ranar Litinin.

Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin da News Point Nigeria ke sa ido.

Ya ce ‘yan takarar jam’iyyar adawa uku a zaɓen da ya gabata – Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labour Party da kuma Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) – za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su ƙulla ƙawance mai ƙarfi don kayar da jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki. APC) 2027.

Abdullahi ya ce da a ce shugabannin jam’iyyarsu na baya sun gudanar da rigingimu da kyau, manyan jiga-jigai kamar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, Kwankwaso da Obi za su kasance cikakkun ‘ya’yan jam’iyyar PDP kuma jam’iyyar ta doke Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a zaɓen da ya gabata.

Ya ce, “Mun yi rashin Kwankwaso, mun rasa Peter Obi, duk waɗannan mutane, ka yi tunanin idan suna cikin jam’iyya, za mu ci zaɓe.

“Wannan APC ta ce sun ci mu da miliyan ɗaya da ƙuri’u, ɗaya daga cikin waɗannan sunaye da na ambata da zai rufe mana wannan giɓin kuma da mun yi mulki a yau, kuma da tabbas ‘yan Nijeriya ba za su fuskanci irin waɗannan abubuwa ba a cikin ƙasar.”

Da aka tambaye shi ko PDP na ƙoƙarin dawo da Obi, Kwankwaso, Wike da sauran su cikin jam’iyyar, Abdullahi ya ce, “Tabbas ana tattaunawa. Za ku ga Peter Obi yana tattaunawa da Atiku, za ku ga Peter Obi yana ganawa da (Nasir) El-Rufai. Gudanar da jam’iyya abu ne mai matuƙar wahala kuma muna yin iyakacin ƙoƙarinmu a cikin ƙuncin da muka tsinci kanmu. Ka tabbata, za a sami haske a ƙarshe. Mun koyi darussanmu ta hanya mai daci.”

A zaɓen Shugaban ƙasa na 2023, Tinubu, ya yi nasara a jihohi 12 daga cikin 36 na Nijeriya, kuma ya samu ƙuri’u masu yawa a wasu jihohi da dama da ya samu ƙuri’u mafi yawa – 8,794,726, kusan ƙuri’u miliyan biyu fiye da na babban abokin hamayyarsa – Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau shida, ya samu ƙuri’u 6,984,520, yayin da Obi, wanda ya tsaya takara karo na farko, ya samu ƙuri’u 6,101,533 da ba a taɓa ganin irinsa ba. Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya zo na huɗu, yana mai iƙirarin nasara a jiharsa – Kano. Ya samu ƙuri’u 1,496,687.

Wani abin sha’awa shi ne, Obi da Kwankwaso ‘yan PDP ne watanni kafin zaɓen da ya gabata amma sun bayyana rashin jituwa a matsayin dalilan da suka sa suka fice daga jam’iyyar.

Da aka tambaye shi ko me zai faru idan Obi da sauran su koma PDP, sai ya ce, “ɗaya daga cikinsu zai yarda ɗayan sannan mu samu alkibla.

“Damuwarmu a matsayinmu na jam’iyya da kuma waɗannan mutanen da na ambata shi ne mu tabbatar da cewa mun ceto ‘yan Nijeriya daga wannan ƙunci da rashin jin daɗi, tsakanin matsalolin yunwa da rashin tsaro da ke damun ƙasa. Kuna iya ganin rashin fahimta da rashin sanin yakamata daga ɓangaren waɗannan mutanen da ke tafiyar da ƙasar nan.”

Jigon na PDP ya ce ceto ‘yan Nijeriya daga cikin wahalhalun da suke ciki ya fi burin kowane mutum ukun.

Ya ce, “Atiku yana cewa idan har ya fi dacewa ya fitar da Nijeriya daga wannan rashin bege, zai yi haka.

“Bai kamata shi (Atiku) ya kasance cikin tseren ba. Atiku yana cewa haƙƙi ne a gare shi a matsayinsa na mai bin dimokraɗiyya; kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar masa cewa zai iya tsayawa takara a kowane lokaci.

“Abin da yake ƙoƙarin cewa shi ne (babu) babu rufin da zai hana shi takara. Wannan shi ne ainihin haƙƙinsa na dimokuraɗiyya amma ba wai yana cewa zai tilasta wa jam’iyya ko ƙasa ba.

“Ina gaya muku sarai: Peter Obi ya cancanta; zai iya buri kuma za mu tallafa masa idan ya samu tikitin. Atiku ya cancanta kuma idan ya samu tikitin, za mu mara masa baya tare da ba shi goyon bayan da ake buƙata domin ceto ‘yan Nijeriya daga halin da ake ciki.”

By ukarofi