Ambaliyar Borno: NCS ta fitar da jaddawalin waɗanda suka tsere daga gidan yari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCS) ta ce aƙalla fursunoni 281 ne daga gidan yarin da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno suka tsere.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ambaliyar ruwan sama da ta auku a birnin inda ta ɗaiɗaita wani kaso mai tsoka na yankin yayin da fursunoni bakwai suka koma kurkukun.

A ranar Lahadi, Kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar da jaddawalin bayanan fursunonin da suka arce.

Ya ce, sun tabbatar da rugujewar wani sashi na ginin kurkukun Maiduguri wanda hakan ne ya sabbaba arcewar wasu daga cikin fursunonin.

Ya bayyana cewa, NCS na ɗauke da dukkanin bayanan wanɗanda suka tseren kuma sun baza su acikin al’umma, ya na mai cewa suna aiki tare da haɗin-gwiwar wasu hukumomi a ƙoƙarinsu sake kamo su tare da mayar da su don cigaba da fuskantar hukuncin da aka yanke mu su.

By Babaji