Gwamnatin Kano ta tada shari’ar wanda ake zargin sa da cinna wuta a masallaci

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

A ranar Talata ne Gwamnatin Jihar Kano ta buɗe takardar shari’arta da wani Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 da ake zargin sa da cinna wa masallaci wuta.

An buɗe shari’ar ne a wata kotun Shari’a (Upper Shari’a Court) inda ake tuhumar sa da laifukan yunƙurin kisa, sabbaba raunatawa da kuma ƙoƙarin tada gobara waɗanda sun ci karo da wasu daga cikin dokokin kundin kotun Shari’a ta Kano da aka fitar a 2000.

Daraktan bincike kan harkokin al’umma na Ma’aikatar Shari’ar jihar, Salisu Tahir ya gabatar da shaidu huɗu inda ɗaya daga ciki, Abdul’aziz Yahaya mai shekaru 55 ya ce, a ranar 15 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 5:45 na safe ya samu labarin an banka wa wani masallaci wuta.

“Yayin da na isa wajen, sai na ga mutane da dama sun ƙone, sai muka hanzarta kai su asibitin Sir Muhammad Sanusi Kano.”

Daga bayan an garzaya da su asibitin Murtala don cigaba da karɓar kulawa.

“Mutane 23 ne suka rasa rayukansu yayin karɓar magani. Daga nan ne sai wanda ake zargin ya kai kansa ofishin ƴan sanda na Gazawa.”

Haka nan wani Aminu Abubakar, 42, wanda wa ne wanda ake zargin ya bayyana wa kotu cewa, an kira shi a ranar 15 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 5:15 inda aka faɗa masa cewa akwai matsala.

Ya ce, mahaifinsu ya rasu tun shekaru 15 da suka gabata kuma an raba musu gadonsu.

Sai dai wanda ake zargin ya samu matsala da ƴan uwan mahaifin nasu wanda a saboda haka ya ji musu raunuka.

Baya ga haka ne “wanda ake zargin ya kai kan sa ofishin ƴan sanda na Hotoro, sai aka ba ni shawara na kai shi asibitin mahaukata da ke Dawanau don a masa magana, kuma an tabbatar ya na da taɓin hankali.”

Alƙalin da ke hukunci kan ƙarar, Halhalatu Zakariyya ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 24 ga watan Satumba.

By Babaji