An sake shi bayan tsare shi
Daga SADIYA SIDIYA a Abuja
Ana zargin wani soja mai muƙamin ‘Last Chopra’ a Abuja mai suna Muhammed Ghanni Danladi da yi wa wasu ƙananan matasa guda biyu ‘yan shekara 16, Sa’id Sidi Sa’id da Ibrahim Ali, wanda ake kira da Imam, dukan kawo wuƙan da ya haifar mu su da mummunan lahanin da ya jikkata su, inda har aka yi tsammanin sun ma rasa rayukansu.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 13 ga Satumba, 2024, a yankin Maraba cikin Ruga ’Yar Kasuwa da ke ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa kan iyakar Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sai dai kuma, bayanai sun nuna cewa, Ghanni Danladi, wanda shi ne mamallakin wata fitacciyar filaza a Maraba daura da Babban Birnin Tarayya Abuja mai suna Afraah Plaza, ya aikata wa matasan wannan aiki ne bisa zargin su da satar ma sa buhun shinkafa guda ɗaya da suka yi a shagon da ya ke sayar da kayan abinci a cikin filazar. Majiyarmu ta ce, sojan, wanda aka yi zargin yana hutun karatun da ya ba shi damar miƙe ƙafa a cikin farar hula ne, maimakon ya kai matasan gaban kuliya, don yi musu hukuncin da ya dace da su, sai ya ɗauki doka a hannunsa, inda a yanzu ake tsammanin ya nakasa lafiyar jikin matasan.
Majiyar Blueprint Manhaja ta shaida mana cewa, al’amarin ya taso ne yayin da ɗanladi ya zo har gidan iyayen yaran da sanyin safiya misalin ƙarfe 7:00 na safe, ya yana neman su cewa, ya ga ɗaya daga cikin yaran gidan a na’urar tsaro yana ɗaukar masa babban buhun Shinkafa.
Ya yi barazanar cewa, tabbas idan iyayen yaron ba su kawo yaron ba zuwa karfe 9:00 na safe, to ko dai a biya shi kuɗin shinkafarsa ko kuma ya kai yaran kotu. Ya ƙara da barazanar cewa, zai iya shiga cikin gidan kanshi tsaye ta inda ya ga dama ya daki duk wanda ya ke so, saboda shi ya na ma zargin ko iyayen yaran sun ɓoye yaran ne da buhun shinkafar.
Iyayen sun shaida Wakiliyarmu cewa, sun nuna masa jimamin faruwar lamarin tare da yin Allah wadai da irin ɗauko musu magana da yaran suka yi, suka yi masa alƙawarin za a je a nemo yaran duk inda suke a kai masa hannu da hannu, saboda kasancewar ba su kwana a gida ba.
A zantawa da iyayen, sun ce shaida wa Blueprint Manhaja cewa, a ranar yaran sun kwana ne a gidan yayarsu sakamakon ba kowa a gidan yayar, saboda ta koma gida tana yin jinya. Don haka su suke kwana a gidan nata.
Daga nan a ka tayar da yayansu da kawunnensu biyu suka je suka tado su daga bacci, suka tambaye su, shin abin da soja mai shagon nan ya faɗi gaskiya ne? nan take su ka ce, “eh” ba tare da sun yi gardama ba. Sai aka tambaye su inda suka kai shinkafar, inda kuma aka tasa ƙeyarsu suka nuna.
Iyayen yaran da hannunsu suka ɗauki yaran da buhun shinkafar suka kai wa mai shagon tare da ba shi haƙuri a bisa kuskuren da yaran suka aikata masa, sannan suka ce ya yi musu hukunci a matsayin duk a na tare, kuma wasu daga cikin yayyen yaran sun yi masa aiki a shagonsa.
Bayanai sun nuna cewa, daga nan sai mai shagon, wanda ya yi iƙararin shi soja ne, ya ɗauki mummunan mataki akan yaran wanda ya zarce ƙa’ida, inda ya yi hayar sojoji guda biyu da ƙarin mutane uku har shi huɗu, suka ɗaure yaran ya yi musu zindir, sannan suka hau dukan su da gora.
Bayanai sun nuna cewa, tun misalin ƙarfe 8:00 na safe suke dukan yaran har 12:00 na rana. Tun ya na dukan su da gora har ta karye, ya sa ƙarfen ‘GOLF’ suka ci gaba da dukan su. Idan yaran suka suma sai ya ɗauko ruwan sanyi ya fasa a jikinsu, sai su farfaɗo, ya kuma ci gaba da dukan su. Tun suna iya yin ihu har aka daina jin kukansu.
Mutanen unguwar sun shaida wa wakiliyar Blueprint Manhaja cewa, babu irin haƙurin da dattawan unguwar ba su ba shi ba, amma bai saurare su ba, sai ya ce shi soja ne ko kashe yaran ya yi, babu abunda zai faru, saboda kakinsa ya ba shi damar ya hukunta duk wanda ya ga dama a ko ma yaya ne.
Bai saurara wa yaran nan ba sai da ya ga ba sa iya motsi, sannan ya sa matasa suka kwashe su suka kai su gidan iyayensu tare da aika saƙon su je su turo duk wanda za su turo zai ga uban da ya tsaya musu, saboda ya ga yaran talakawa ne.
Wannan lamari ya tayar da hankalin iyayen yaran da jama’ar unguwar da ma garin bakiɗaya, wanda a sanadiyyar ganin yaran ba sa motsi ya sa aka yi tunanin ko sun mutu ne, aka yi dandazo za a ƙona shagonsa da ma shi kanshi sojan. Wannan ya janyo hankalin jami’an ’yann sandan yankin, waɗanda suka shiga tsakani, waanda suka tusa ƙeyar ɗanladi har aka tafi da shi zuwa asibitin da aka kai matasan.
A yayin zantawa da mutanen unguwar, sun shaida mana cewa, ba wannan ba ne yinsa na farko. A lissafi su ne yara na takwas da ya yi wa makamancin irin wannan hukuncin, har da yara ƙanana da ba su ma haura shekaru 10 ba ya sha duka idan aka taɓa abinsa, kuma komai ƙanƙantar abin ko ƙanƙantar wanda ya taɓa abin ba ya duba wannan.
Bayanai sun nuna cewa, jimm kaɗan bayan hakan ne wani daga cikin dangin yaran ya garzaya zuwa Abacha Barracks, don kai kuka ga rundunar sojoji bisa halin da ake ciki.
Sakamakon yadda mutanen yankin suka hasala suka yi tururuwa zuwa asibitin da aka kai yaran, don afka wa Soja ɗanladi, ’yan sandan sojoji da suka iso wajen ne suka damƙe ɗanladi a harabar asibitin tare da alƙawarin ɗaukar matakin da ya dace, don kwantar da hankalin jama’a.
Bayan ya shiga hannun jami’an tsaro, jama’ar yankin sun yi ta iƙirari da yekuwar cewa, “shi ma ai ɓarawo ne!” A cewarsu, shi a ina ya ke samun kuɗaɗen da ya mallaki kadarorin da ya mallaka, saboda a saninsu mai irin matsayinsa a irin aikin da ya ke yi ba zai iya tara irin wannan kadarorin ba.
Bincike ya tabbatar mana muƙaminsa a aikin soja shi ne, ‘Last Chopra’ ne, ma’ana matakin kusa da ƙarshe na ƙasa, wanda su ke zargin albashinsa ba zai mallaka masa irin wannan tarin kadarorin ba.
A binciken da muka yi, an tabbatar mana ya na da fulazozi, gidajen haya da kuma shagunan kansa da ake gudanar masa da kasuwanci. Sun ƙara da cewa, inda ya ke ba garinsu ba ne, ba ƙabilarsa ba ne, ba kuma yarensa ba ne, amma duk da haka saboda girammawa suke tsallake ‘yan uwansa Hausawa su na siyayya a wurinsa, amma wannan bai sa ya ga mutuncinsu ba ko ɗaga wa yaransu ƙafa da ke kai kawo wurin kula masa da dukiya.
An kulle shi a barikin sojoji na Abacha Barrack da ke Abuja, wanda aka canza wa suna yanzu zuwa Mogadishu Barrack. Amma duk da haka iyaye, ‘yan uwa da jama’ar wannan yanki suna neman a bi musu haƙƙin ‘ya’yansu. A yanzu yaran na asibitin cikin barikin a ƙarƙashin kulawa ta musamman daga likitoci.
Sai dai kuma mu na dab da kammala haɗa wannan rahoton, mun samu bayanan cewa, an sako Ghanni ɗanladi, kodayake duk ƙoƙarin da Blueprint Manhaja ta yi na jin ta bakin hukumomin soja ya ci tura.


