Ban zo shugabanci don kuɗi ba – Shugaba Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba wai ya na shugabantar Nijeriya ba ne don neman wata riba ko tara dukiya.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da tawagar tsoffin shugabannin Majalisar Ƙasa a lokacin da suka kai masa ziyara Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya na mai cewa ya na kan karagar mulkin ne don yin aiki wa Nijeriya da ƴaƴanta.

Ya ce, duk da ƙalubale da ƙasar ke fuskanta, gwamnatinsa na cigaba da ƙoƙari wajen ganin an samu kyawawan sakamako da kuma sauyi mai amfani a ɓangarorin ababen more rayuwa, abinci, lantarki, ilimi da kuma haɓakar tattalin arziƙi mai ɗorewa.

Tawagar, wacce tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Ken Nnamani ya jagoranta, ta samu halartar mambobi 15 da suka haɗa da shugabannin majalisa, Kakakin majalisa, wakilai, dattijai da sauran su.

Shugaban ya kuma yaba wa mambobin tawagar kan taimako da ƙwarin-gwiwa da su ke bashi duk da bambance-bambancen jami’iyya wajen ganin ya cimma kyawawan manufofin gwamnatinsa ga Nijeriya da al’ummarta baki ɗaya, ya na mai kira a gare su da su ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin-kai da ke tsakanin su.

Bugu da ƙari, la’akari da sarƙaƙƙiya da ke tattare da Majalisa da dokokin ƙasa wajen gina ƙasar, Shugaban ya ce ya na da yaƙinin cewa Nijeriya za ta kai ga nasara ta hanyoyin haɗin-gwiwa da kuma damawa da kowane ɓangare.

By Babaji