PDP ta koka kan zargin katsalandan a tattara sakamakon zaɓen Edo

Spread the love

Shugaban yaƙin neman zaɓen Gwamnan Jihar Edo, kuma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, na jam’iyyar PDP, ya fitar da sakamakon da ya samu a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

Fintiri wanda ya karanta wa ‘yan jarida sakamakon a wani taron manema labarai a birnin Benin, ya ce; “Duk wani abu da za ayi bayan wannan zai kasance ba bisa ƙa’ida ba, ya zama cin zarafi ne da son rai da cin mutuncin dokar zaɓe ta 2022.”

Gwamna Godwin Obaseki (Edo) Sheriff Oboriworhe (Delta) da Agbu Kefas (Taraba), sun kasance tare a daidai lokacin da yake ya ke karanta sakamakon.

Ya kuma bayyana damuwarsa da cewa an katse bayyana sakamakon a ƙananan hukumomi da dama a faɗin jihar.

Fintiri ya ƙara da cewa: “A Edo ta Kudu, an dakatar da ayyukan tattara sakamakon ƙananan hukumomi a Oredo, Ikpoba-Okha, da Egor, aka koma hedikwatar INEC ta jihar wanda hakan ya saɓa ka’ida.

“Sai aka umarci wakilan jam’iyyar da abin ya shafa da su hallara a hedikwatar hukumar ta INEC da ke Aduwawa a ƙaramar hukumar Ikpoba Okha domin kammala aikin tattara sakamakon.

“Da isar wakilan jam’iyyar PDP ba a ba su izinin shiga ofishin INEC na jihar domin gudanar da aikin ba.

“A ɗaya ɓangaren kuma, an baiwa wakilan jam’iyyar APC damar shiga harabar hukumar ta INEC ba tare da wata tangarɗa ba don shiga cikin shirin.”

By ukarofi