
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jagorantar zaman Majalisar Zartarwa (FEC) a ofishinta na Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A na gudanar da zaman ne wanda rahotanni mabanbanta ke nuna cewa akwai yiwuwar a samu garambawul acikin jagororin gwamnatinsa.
Tinubu, wanda ya sha alwashin sallamar duk ministan da aka ga ya gaza wajen sauƙe nauyin da aka ɗora masa, ya yi gum game da maganar sauyi a cikin ma’aikatan gwamnatin nasa.
Gabannin zaman, Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarinsa na tabbatar da an yi zaɓen gwamnan jihar Edo cikin lumana.
Ya yaba wa shugabancin jam’iyyar APC na Edo ganin yadda suka taimaka wajen samun nasarar Sanata Monday Okpebholo na jami’yyar.
Akume, ya kuma sanar da batun mutuwar tsohuwar Ministar Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci-gaban Matasa, Mrs Salome Jankada da ya faru a ranar 27 ga watan Agustan shekarar nan wacce ta yi aiki a zamanin tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo.
Cikin mahalarta zaman akwai; Sanata George Akume; Shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da kuma Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
