Obaseki ya magantu bayan INEC ta sanar da nasarar ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Edo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da ƙaurace wa tashin-tashina da lalata dukiyoyin al’umma.

Obaseki ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da manema labarai bayan hukumar zaɓe, INEC ta sanar da Monday Okpebholo na jami’yyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar.

A ranar Lahadi ne INEC ta sanar da nasarar ɗan takarar APC’n duk da cewa akwai zargin maguɗi a zaɓen.

Ɗan takarar ɓangaren gwamnan Asue Ighodalo shi ya zo na biyu inda Obaseki ya ce an yi zaɓen tare da take wasu dokoki wanda a sakamakon haka, akwai yiwuwar su shigar da ƙara a kai.

By Babaji