Daga USMAN KAROFI
Babbar kotu a Jihar Kano wanda mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ke jagoranta ta dakatar da aƙalla jam’iyyun siyasa 19 daga shiga zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.
Umarnin koton kamar yadda hukumar zaɓe ta jihar ta buƙata shine hana jam’iyyun yin katsalandan a zaɓen a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin kano.
Mai ƙara itace hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano. Sai kuma waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam’iyyu kamar su , People Democratic Party (PDP), Accord Party( AP), All Progressive Congress ( APC) da sauran su.
Alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa 10 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraren shari’ar.
