Daga USMAN KAROFI
A wata sanarwa da jakadan ƙasar Falasɗinu ya fitar ta shafinsa na X, ya bayyana matuƙar godiya ga ƙasar Nijeriya bisa zaɓen da ta yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na cewa Falasɗinu na da yanci kamar kowacce ƙasa a duniya.
Abdallah M Abu Shaweesh ya cigaba da bayyana irin munafunci na ƙasashen yamma dangane da lamarin yancin Falasɗinu.
Ya nuna takaici game da Kotun manyan laifuka ta duniya ta gaza yin komai a kan laifukan keta haƙƙin bil’adama, a cewar su an yi kotun ne domin hukunta laifuka daga Rasha da Afirka.
A cikin jawabin na shi, ya ƙara da bayyana alƙaluma na mutanen da suka rasa rayukan su daga munanan hare-hare da Isra’ila ke kaiwa a zirin Gaza.
Ya zuwa ranar Litinin, aƙalla Falasɗinawa 10,600 ne suke a tsare a matsayin fursunoni a ƙasar Isra’ila yayin da aƙalla mutane 41,467 ne su ka rasa rayukan su a West Bank da wasu ma’aikatan jin ƙai aƙalla mutum 222 da su ma su ka rasa ransu.
Daga ƙarshe ya yabawa Nijeriya bisa matsayin da suka ɗauka a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na ganin cewa Falasɗinu sun kasance cikin yanci.
