Ƙungiyar Matan Kannywood sun fice daga Kwankwasiyya zuwa tafiyar Sanata Barau Jibril

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A daina lokacin da yanayin siyasar ƙasar nan yake sauya sabon salo na kama abokin tafiyar da za a gudu tare a tsira tare, su ma a cikin harkar siyasar Kannywood haka abin yake ta yadda kowa yake neman hanyar da za ta ɓulle masa.

Koda yake sauya sheƙar siyasa a wajen ‘yan fim ba wani sabon abu ba ne saboda kallon da ake yi musu na ‘yan kasuwar siyasa. 

Sai dai kuma a wannan lokacin abin ya zo da wani sabon salo da zai bayar da mamaki ga masu lura da siyasar Kannywood da kuma kallon da ake yi musu na masu kyakkyawar alaƙa da Gwamnatin Jihar Kano ta Kwankwasiyya, ganin yadda gwamnatin take cike da ‘yan fim a cikin ta da suke riƙe da muƙamai.

Amma dai a salon tafiyar siyasar ƙungiyar Matan Kannywood da Hajiya Zulai Muhammad Bebeji take jagoranta a cikin tsarin Kwankwasiyyar ba haka abin yake ba, domin kuwa duk abubuwan da suke faruwa tana jin labari ne kawai ita da mutanen ta, domin ba ta san ma ana yi ba, duk da shekaru masu yawa da suka shafe suna hidimar su ga tafiyar, amma da aka kafa gwamnati sai wasu masu shan kai suka hana su damar zuwa wajen da za a gan su a ji koken su har ma a san da su. Don haka suka yanke hukuncin barin tafiyar Kwankwasiyya tare da komawa APC a ɓangaren Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibril.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai ƙungiyar Matan Kannywood da Hajiya Zulai Muhammad Bebeji take jagoranta suka samu gayyata daga Ofishin Sanata Barau Jibril da ke Abuja, inda suka je domin gabatar da kansu a matsayin waɗanda suka rungumi tafiyar sa tare da sanar da shi manufofin su da kuma ƙarfin da suke da shi da kuma gudunmawar da suke bayarwa a cikin harkar siyasa wadda ta taimaka wajen samun nasarar Gwamnatin Jihar Kano ta Abba Kabir Yusif a wajen samun nasarar sa.

Hajiya Zulai Muhammad Bebeji ta ce, “Amma duk da haka ba a ga irin ƙoƙarin mu ba don haka ne muka ga zaman mu a wajen ba shi da amfani.”

“A lokacin da aka gammu ana cire mana jan mayafi za wasu ma za su ce wannan kuma me ta yi a tafiyar Kwankwasiyya. Amma dai mun yi tafiya ta Kwankwasiyya, mun kai mun komo wajen bayar da gudunmawa da ƙarfina da kuma ƙungiyar da nake jagoranta. Amma dalilin da zai sa ba a sanni ba, shi ne waɗanda nake yi wa ƙoƙarin ba su yarda sun kaini inda za a ga abin da nake yi ba, don haka kullum nake yin tsalle ina direwa a waje ɗaya. Don ina tabbatar maka na yi tafiyar Kwankwasiyya tun a 2019, kuma duk abubuwan da suka faru da mu aka yi, wanda kowa ya san abubuwan da suka faru wanda aka murɗe zaɓen. Kuma haka muka ci gaba da tafiya har aka zo wannan lokaci da Allah ya sa muka kafa gwamnati, wanda muke ganin tamu ce. Amma yadda muke da mutanen da muka shafe tsawon lokaci muna hwagwarmayar da su a yanzu sai suka yi mana katanga da gwamnatin yadda za a ji a ga ƙoƙarin da muka yi, don haka duk wani abu da za a yi sai ya zama an mayar da mu gefe, idan ma wani abu ne ya taso za a yi da ‘yan fim mu sai dai mu ji ana yi. Kuma duk abubuwan da za mu yi na ci gaban wannan gwamnati idan mun kawo sai waɗannan mutanen su hana mu kai inda ya kamata a ji a san da mu. Wannan ta sa na ga ba a damu da mu ba, ba a ma san da zaman mu ba, dole ne mu nema wa kanmu mafita.

Don haka ne muka koma tafiyar APC gidan Sanata Barau Jibril, domin mun ga ya na da son ci gaban Jihar Kano da ƙasa bakiɗaya kuma muka je ofishinsa a Abuja ya karɓe mu hannu biyu ya yi mana alƙawarin kulawa da mu tare da jin ra’ayin mu na siyasa domin akwai gudunmawa da za mu bayar. Kuma mu ma mun yi masa alƙawarin tafiya tare da kuma bayar da gudunmawa ta duk inda ake buƙata. Don haka mu a yanzu ƙungiyar Matan Kannywood tafiyar Satana Barau Jibril muke yi ita za mu yi, saboda manufofin sa na ci gaban rayuwar al’umma sun yi daidai da manufar tafiyar ƙungiyarmu. Muna fatan Allah ya yi mana jagora ya kawo mana ci gaba a Jihar Kano da ma ƙasa bakiɗaya,” a cewar ta.

By ukarofi