Tinubu ya bada umarnin kafa asusun agajin gaggawa don daƙile afkuwar bala’o’i

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kafa asusun agajin gaggawa domin magance ambaliyar ruwa da sauran iftila’i.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya ce shugaban ƙasar ya bayar da wannan umarni yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a ranar Litinin, 23 ga Satumba, 2024.

Ya ce bisa la’akari da cewa bala’o’i kamar ambaliyar ruwa na Maiduguri za su zama ruwan dare gama gari saboda sauyin yanayi, akwai buƙatar a samar da kuɗaɗe na musamman don tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

Aƙalla mutane 400,000 ne suka rasa matsugunansu, sannan 100 suka mutu a bala’in ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri a farkon watan nan.

A yayin ziyarar da ya kai jihar, Tinubu ya sanar da wani asusun bayar da agajin gaggawa don taimakawa ‘yan Nijeriya da ambaliyar ruwa da wasu bala’i suka shafa.

Tinubu, wanda ya buƙaci ’yan kasuwa masu zaman kansu da su bayar da tasu gudunmuwar a cikin asusun, ya ce irin wannan shiri yana da amfani saboda ba a san irin aftila’in da za ta afku a ba a nan gaba daga yakunan ƙasar nan.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin mai take, ‘Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Borno, ya yi alƙawarin aara tallafawa ‘yan ƙasa, samar da asusun tallafa wa waɗanda bala’i ya shafa.

Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, wanda ya raka shugaban ƙasar a ziyarar, ya ce majalisar za ta haɗa kai da ɓangaren zartarwa domin kafa asusun.

Tinubu ya ziyarci Shehun Borno sansanin ‘yan gudun hijira a makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Maiduguri inda ya zagaya yankunan da bala’in ya shafa.

By ukarofi