‘Yancin-kai (Independence)

Spread the love

Daga MUHAMMAD BALA GARBA

  1. Gobe ranar Independent,
    Wahala ba mu daina sha ba.
  2. Shekaru sittin da ɗori,
    Ba mu sauya ginin ƙasar ba.
  3. Ga shi ƴanci aka ba mu,
    Bautuwa ba mu daina yi ba.
  4. Ilimi an kassara shi,
    Rashawa ba a bar batun ba.
  5. Ba ruwan sha babu NEPA,
    Me ya sa ba zan koka ba?
  6. Babu noma babu kiwo,
    Ba mu san daɗin ƴanci ba.
  7. Lafiya an wargaza ta,
    Shi ya sa ba zan murna ba.
    1. Ga shi fetur na ta tashi,
      Ga shi ba noma muke ba.
    2. Ga abinci yana ta tsada,
      Ba a ƴan salari muke ba.
  8. Ga matasa babu aiki,
    Kuma gwamnati ba ta kula ba.
  9. Ba tsaro birni da ƙauye,
    Ba mu san sanadin hakan ba.
  10. Sai a saci uwa da ƴarta,
    Har da Sarki ba a bari ba.
  11. Matsaloli sun yawaita,
    A ƙasarmu gidan su Baba.
  12. Ajalinmu yana matsowa,
    Ga ƙasar ba ta ɗau saiti ba.
  13. Babu ƙarfi babu ƙarfe,
    Ga shi ƴaƴa ba su tasa ba.
  14. Ciki zafi waje ƙuna,
    Ban ga amfanin ƴanci ba.
  15. To ina zance na murna?
    Tun da ba ƙoshi muke ba.
  16. Me ya sa ma zan yi murna?
    Ga hawaye bai tsaya ba.
  17. To ina hujja na murna?
    Ɗalibai ba a bar sata ba.
  18. Me akai har zan yi murna?
    Tallafi ba a mai da shi ba.
  19. Shin ta yaya zan yi murna?
    Ba a daina kisan kawai ba.
  20. Babu amfani na murna,
    A ƙasar da ake ta zamba.
  21. Masu murna kuy abin ku,
    Ɗan-Bala ba zai hakan ba.
  22. Rabbana kai mana sauyi,
    Don Rasulu ba Ka ƙi yi ba.
  23. Rabbi ceci ƙasarmu Allah,
    Don ba za Ka ƙi yin hakan ba.
  24. Zan tsaya haka zana huta,
    Ba ƙiyayya ni nake ba.
  25. Na rufe da dubun salati,
    Gun Habibu riƙon Suwaiba.
  26. Alihi nasa har Sahabu,
    Ambatonsu ba zan ƙi yi ba.
  27. Ɗan-Bala ya rubuta waƙar,
    Can a Borno ba zan ɓoye ba.
  28. Baituka linta na tsara,
    Don ba zan yi shuru a kai ba.

©️
Mohammed Bala Garba.
5:29pm
1 Oktoba, 2022.
Sabuntawa
12:31pm
30 Satumba, 2024.

By Babaji