Gajeren labari da dogon labari dukansu abu guda suka ƙunsa – Fauziyya Sani Jibril 

Spread the love

Dalilin rubutu na san manyan mutane

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

MANHAJA: Wanne abin farinciki ko akasin haka ne ya taɓa faruwa da ke ta sanadiyyar rubutu wanda ba za ki manta da su ba?

FAUZIYYA: Gaskiya abubuwan suna da yawa, daga ciki akwai yadda na ji daɗin kasancewa ta a cikin marubuta, saboda zumunci da kuma karamcin da suke da shi. Bugu da ƙari duk da ban daɗe sosai a zauren marubata ba, ga kuma tarin ƙwararrun marubuta, amma a hakan na samu nasarar zama Gwarzuwa a gasanni har guda biyu, wanda tazarar gasannin ba ta fi ta ‘yan watanni ba, haƙiƙa wannan abin farinciki ne a gare ni da ba zan taɓa mantawa da shi ba.

Dalilin rubutu na san manyan mutane, manyan marubuta waɗanda ba don dalilin rubutu ba, da ban san su ba. Kuma na sha samun kyaututtuka daga masu karanta labaraina, da kuma yabawa daga Manazarta. Kyaututtukan da na sha samu, sun haɗa da kyautar kuɗi, katin waya, data, da lambobin yabo daga ɓangarori da dama. Haka kuma an sha gayyata ta a yi hira da ni a matsayina na Marubuciya. An yi hira da ni a ƙungiyarmu ta Lafazi Writers Association, a shirin da ake gabatarwa duk sati na Mu San Juna, wanda Malam Abubakar Sadik da Asiya Muhammad suke gabatarwa. An yi hira da ni a gidan rediyon Dala FM cikin shirin Duniyar Marubuta wanda Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano yake gabatarwa a duk ranar Talata. An yi hira da ni a jaridar LeadershipHausa, a filin Adon Gari, wanda Aunty Bushira Nakura take gabatarwa. Bugu da ƙari kuma ga hirar da ake yi da ni a yanzu, a jaridar Manhaja cikin shafin Adabi, tare da Malam Abba Abubakar Yakubu, wanda hakan ba ƙaramar nasara ce a gareni ba. Kuma duk waɗannan tarin abubuwan farinciki ne da ba zan taɓa mantawa da su ba. Alhamdulillah.

Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu a kai?

Ina samun jigon da nake rubutu a kai ne ta hanyar duban abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, musamman waɗanda na ga suna da buƙatar a wayar da kan al’umma a cikinsu. Ko kuma idan na ga wani abu ya faru wanda ya kamata a yi kira ko tunasarwa a kansa. Ko kuma wani lamari da na ga yana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya, sai na ɗauke shi ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan na gina labari a kai. Kuma nakan ɗauki abin da ya faru a gaske na rubuta shi a matsayin labari, wato True Life Story. 

Wanne salon rubutu ne ya fi baki sha’awa, almara, yaƙe-yaƙe, sarauta, ko soyayya?

Salon labarin da ya fi ba ni sha’awa shi ne labarin da ya shafi zamantakewa, musamman a taɓo ɓangaren al’adu da kuma soyayya. Domin al’adunmu su ne gadonmu, sako su cikin labari zai sa a daɗa sabunta su, kuma al’umma za su ƙara yin riƙo da su. Haka kuma al’adu musamman kyawawan cikinsu suna da matuƙar burgewa da ban sha’awa tare da tasiri a rayuwar al’umma. Ita kuwa soyayya mahaɗin rayuwa ce, indai akwai rayuwa to, tabbas akwai soyayya, don haka ba a raba rayuwa da soyayya.

Wanne labari ne ya fi baki wahalar rubutawa ko ki ka fi jin sauƙin rubutunsa?

Gaskiya a wajen rubutu na fi son rubuta gajeren labari, kuma na fi jin daɗi da nishaɗi idan ina rubuta shi. Dogon ma ina jin nishaɗi yayin rubuta shi, amma gaskiya ba kamar gajeren labari ba. Ina son rubuta gajeren labari ne saboda shi gajeren labari da dogon labari dukansu abu guda suke ƙunshe da shi, yadda dogon yake fito da abin da ake son nuna wa al’umma, haka gajeren yake fito da komai ƙuru-ƙuru. Kawai bambancin da yake tsakaninsu abubuwa ne guda biyu, bin gajeriyar hanya da kuma doguwa, sai kuma yawan kalmomi. Kuma yawan rubuta gajeren labari yana sakawa a ƙara gogewa sosai wajen iya tsara labari.

Amma a ɓangaren salo, babu salon da yake ba ni wahala wajen rubutu a kansa, domin kowane irin salo idan na tashi yin rubutu da shi sai na nemi kyakkyawan jigo, sannan na yi bincike sosai a kan jigon, da zarar na fitar da ƙwarangwal ɗin labari to, shi kenan sai zaren labarin ya miƙa.

Wacce ɓoyayyiyar baiwa ki ke da ita wacce ba kowa ya sani ba a cikin marubuta?

(Dariya) To, wannan baiwar da ka ke tambaya ba ta wuce baiwar rubuta waƙa ba. Allah Ya yi min basirar rubuta waƙoƙi, sai dai waƙoƙin yabon manzon Allah (SAWA), kaɗai nake rubutawa. Kodayake, ina rubutawa amma ba na rerawa, sai dai idan na rubuta yara nake bai wa su rera a wajen Mauludi a matsayin ƙasida. A yanzu kuma idan tunanin rubuta waƙar ya taso min, sai na tura wa Malam Aliyu Usman Al’usku ya duba mini ita tare da yi mini gyare-gyare kafin a rera ta.

Wane ne ya fi taimaka miki wajen sanin ƙa’idojin rubutu, don inganta labarinki?

Waɗanda suka fi taimaka mini wajen sanin ƙa’idojin rubutu, don inganta labarina, sun haɗa da shugaba Malam Abubukar Sadik, jagoran ƙungiyar Lafazi Writers Association, ya koyar da ni sanin ƙa’idojin rubutu yadda ya kamata, da kuma hanyoyi da dabarun da ake bi wajen tsara labari dogo da gajere. Sai kuma Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano, shi ma ya taka muhimmiyar rawa, wajen koyar da ni ƙa’idojin rubutu, da hanyoyi gami da dabarun rubuta labari, musamman gajeren labari, a wani zaurensa mai suna Aji Na Musamman.

Sai kuma zauren da Bamai Dabuwa ya buɗe wa Marubuta, a manhajar Whatsapp. Wannan zaure shaƙundum kenan, domin ya tattare komai da komai na cigaban adabi, domin a cikinsa ne ake gabatar da shirye-shirye iri-iri waɗanda suke taimaka wa marubuta wajen ƙara gogewa da ƙwarewa a fagen iya tsara kowanne irin labari.

Shin kina da sha’awar rubutun fim, na wasan kwaikwayo? Ko akwai wani labarinki da aka mayar fim?

Ban taɓa rubuta labarin da aka juya shi zuwa fim ba, kuma gaskiya a yanzu dai ba ni da sha’awar rubutun fim, amma ban sani ba ko nan gaba, tun da komai nufi ne na Ubangiji. 

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wacce gudunmawa take baki ga cigaban rubutunki?

ƙungiyata ta marubuta ita ce, Lafazi Writers Association. ƙungiya ce da take da ƙai’doji da tsare-tsare masu kyau da nagarta, a cikin ƙungiyar ne shugabanmu na ƙungiyar, Malam Abubakar Sadik yake koyar da mu rabe-raben Adabi da kuma ƙa’idojin rubutu. A ƙungiyar ne na samu horo na sanin ƙa’idojin rubutu sosai, da kuma sanin hanyoyin da ake bi wajen gina kyakkyawan labari, tare da dabarun da ake bi don inganta labari.

Kin taɓa shiga wata gasar marubuta, wanne sakamako ki ka samu?

Na taɓa shiga gasanni daban-daban, na samu nasarori masu yawa, daga ciki akwai ita kanta samun damar shiga gasar, na samu nasara a gasar wata-wata ta zauren Marubuta, inda na zama gwarzuwar watan Agusta na shekarar 2023, inda na samu nasara da labarina mai suna ‘Maula’. Haka kuma na ƙara samun nasara a gasar zauren Marubuta mai taken Bincike, wacce aka gabatar da ita yayin bikin cikar zauren shekara bakwai, a ranar 29 ga watan Yuni shekara ta 2024. A wannan gasar na samu nasarar zuwa ta uku da labarina mai suna ‘Tuwon Tulu’, cikin izinin Allah. An kuma buga labaran da suka yi nasara a wani kundin littafi mai suna ‘Abin Cikin ƙwai’. Sannan an yi mini kyautar kuɗi da satifiket. Na kuma taɓa cin gasar musabaƙar Alƙur’ani Mai Girma, wanda aka yi a Zauren Majalisar Marubuta, na samu nasarar zuwa ta biyu, na samu kyautar data da satifiket. A duk gasannin nan da aka yi na samu kyaututtuka da shaidar karramawa. A yanzu haka akwai manyan gasanni da na shigar da labaraina, kuma cikin izinin Allah sun fito a zangon farko na wasu daga cikin gasannin. Ina fatan samun nasara a zangon ƙarshe da yardar Allah, bisa alfarmar Sayyadi Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam.

Wane ne madubin kwaikwayonki a cikin marubuta, maza ko mata?

Duk wasu ƙwararrun marubuta madubin kwaikwayona ne, domin da na gaba ake gane zurfin ruwa, ta hanyar duban yadda na gaba suke tafi da al’amuransu, kan sa mutum ya gyara, ko kuma ya tsara tasa tafiyar, idan mutum ba ya duba rayuwar manyansa, ba zai samu damar yin koyi da kyawawan abubuwa a cikin al’amuransa ba, sai dai ya yi ta badan-badan a wuri guda. Don haka ina da maduban kwaikwayo a cikin manyan Marubutan da nake yawan karanta littattafansu. Daga cikin su akwai: Baba Ado Ahmad Gidan Dabino, Malam Abdullahi Hassan Yarima, Aunty Fauziyya D. Sulaiman, Aunty Halima K/Mashi, Aunty Billy, Malam Jibrin Adamu Rano, Malam Abubakar Sadik, Malam Nura Abu Othaymeen, Malam Muttaƙa A. Hassan, Bamai Dabuwa, Oga Abba Abubakar Yakubu, da kuma Hassana Labaran ɗanlarabawa, Nana Aisha Hamisu, Amira Soley, Aisha Adam, Maryam Sani, da dai sauran su. Duk na koyi abubuwa a wajen su, da suka taimaka min a rubutuna, kuma har yanzu ina kan koya. 

Wanne abu ne kike ganin idan kin samu dama za ki iya yi don kawo canji a harkar rubutun adabi?

Abin da nake ganin zan iya yi idan na samu dama, a harkar adabi don kawo cigaba, shi ne kafa wata ƙungiya mai ƙarfi da za ta dinga hukunta duk marubutan da aka same su da yin rubutun da zai gurɓata tarbiyyar al’umma, ta hanyar cin tarar su, ko dakatar da su. Domin kamata ya yi a ce marubuci ya zama silar gyaruwar tarbiyya ko kyautatuwarta, ba ya zama mai gurɓata tarbiyya ko koyar da wata ɓarna ba. Har ila yau ina da burin tallafa wa marubuta idan Allah Ya ba ni dama, ta hanyar saka musu gasa lokaci zuwa lokaci, tare da bayar da awalaja mai kauri, domin bunƙasa rubutun adabi da cigaban marubuta. 

Mene ne babban burinki nan gaba a harkar rubutu?

Babban burina a duniyar marubuta shi ne, na zama shararriyar marubuciyar da take kawo abubuwan cigaba a duniyar marubuta, da ma al’umma bakiɗaya, ta hanyar rubuta abubuwan da za a fa’idantu da su. Da kuma tallafa wa na ƙasa da ni, kamar yadda ni ma na sama da ni suka tallafa mini.

Wanne karin magana ne ke tasiri a rayuwarki?

Karin maganar da yake tasiri a rayuwata shi ne, samu da rashi duk na Allah ne. Sai kuma ina jindaɗi idan na ji ana cewa, Arziƙin Farin Jakada Muke Ci.

Masha Allah. Mun gode.

Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.

By ukarofi