
Daga BELLO A. BABAJI
Ana tilasta yara a ƙasar Palastine cigaba da kwana a ƙasa inda su ke fafutukar samun nitsuwa don jin labarai kafin yin bacci wanda an ɗauki tsawon lokaci ba samu ba.
Shugaban ofishin jakadancin Palestine, Abdullah Abu Shawesh ya ce kwanaki 363 kenan da ake rugugin wuta a ƙasarsu wanda hakan ya sabbaba mutuwar mutanen da ba su gaza 41,616 ba da raunata 96,359 wanɗanda mafi yawancin su mata ne da ƙananan yara.
Ya ce, aƙalla iyalai 902 ne aka cire daga jaddawalin rijistar ƴan ƙasar ta Palestine.
Rahoton ‘Human Right Watch’ ya ce, zuwa ranar 16 ga watan Satumba, mutanen Palestine 38 ne suka mutu saboda rashin samun isasshen abinci da abin sha waɗanda galibin su yara ne.
A Gaza, sama da mutane miliyan ɗaya ne ba a ba su abinci ba a watan Agusta wanda hakan ya faru ne sakamakon rashin damar isa inda mutanen su ke saboda rashin tsaro da damejin da aka yi wa hanyoyi.
Akan haka ne Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana ƙasar Isra’ila a matsayin wacce ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi wanda hakan ya saɓa wa dokar ƴancin yara. A sakamakon haka, Isara’ila ta haramta wa Sakataren shiga ƙasar ta.
Jakadan ya ƙara da cewa, duk da kira da kotun adalci ta ƙasa-da-ƙasa ta yi na a kawo ƙarshen kai makamai Isra’ila da ababe masu kama da su wanda MƊD ta tabbatar, sai ga shi a ranar 13 ga watan Satumba, Isra’ila ta ce ta samu agajin Dala biliyan 8.7 daga Amurka a matsayin tallafi ga ƙoƙarin dakarun sojojinta da samun fifikon jami’an sojoji a yankin.
