Bikin ‘yancin kai: Jihar Kebbi ta ɗauki ɗumi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

An kashe Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi:

A bikin ‘yancin kan Nijeriya, rahotanni daga ƙaramar Hukumar mulki ta Suru da ke Jihar Kebbi sun bayyana cewa waɗansu da ba san ko su wane ne  ba ne sun afka gidan Shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar mulkin Alhaji Bala Bako Takalafiya inda suka yi awon gaba da shi da kuma ɗansa mai suna Hambali cikin daren Talatar da ta gabata.

Wata majiya daga garin ɗakingari ta bayyana wa wakilinmu da cewa waɗansu mutane ɗauke da bindigogi ne suka shiga gidansa suka ɗauko shi tare da ɗansa mai suna Hambali suka biyo hanyar Kamba.

A daidai ƙauyen Dogondaji suka harbe shi a ƙafa bayan da suka ga ‘yan sa kai sun kusa kama su, shi kuma ɗan sa Hambali suka duke shi suka yar da shi a a jeji suka gudu wanda yanzu haka yana asibiti.

Majiyar ta bayyana cewa an garzaya da Bala Bako zuwa babbar asibitin gwamnatin tarayya ta FMC da ke Birnin Kebbi inda a nan ya rasu ranar Laraba sanadiyyar harbin bindiga.

Wata mai kama da wannan, wata majiya da ba a tantance ba ta labarta cewa kwanan nan ma waɗansu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Matseri da ke ƙaramar hukumar mulki ta Bunza inda suka harbi wani matashi wanda yanzu haka yana kwance a asibitin FMC yana karɓar magani.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar inda Kakaakin rundunar Sufurtandan ‘yan sanda Nafi’u Abubakar ya ce idan ya bincika zai yi bayani sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai kira ba.

Wannan yankin dai ya daɗe yana fama da salon ɗauki ɗai-ɗai da masu garkuwa da mutane ke yi domin karɓar kuɗin fansa.

Gwamnan Kebbi ya raba wa sarakuna motocin alfarma:

Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu ya raba wa manyan sarakuna huɗu da da ke akwai a jihar motocin alfarma ƙirar Toyota Land Cruiser. 

Da ya ke miƙa makullan motocin ga sarakunan, Gwamnan ya bayyana cewa bayar da motocin ya biyo bayan la’akari ne da gwamnatin jihar ta yi na ƙoƙarin da sarakunan ke yi wajen wanzar da zaman lafiya a masarautunsu ta ɓangarori daban-daban.

Gwamnan ya ƙara da cewa wannan gwamnatin ba wani ɓangaren da za mayar shanuwar ware wajen bayar da haƙƙoƙan da suka rataya a wuyanta. 

Idan ba a manta ba, ba da daɗewa ba aka bai wa ‘yan majalisun zartaswa da kwamishinoni da shugabannin rassan waɗansu ma’aikatu da kuma jami’an tsaro motoci. Yau kuma ga shi Allah ya kawo mu ranar da su ma sarakuna aka ba su.

Ba shakka duk mai hankali ya san irin rawar da sarakuna ke takawa musamman wajen wanzar da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan wanda ya a isa a jinjina musu, bisa ga wannan dalilin ya sanya aka ba su irin motocin da gwamna ke amfani da su wanda ba ƙaramin karramawa ba ne.

Ya ƙara da cewa wannan gwamnatin ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman shawarwari daga sarakuna saboda su ne iyaye da suka fi kowa sanin matsaloli tare da hanyoyin warware su.

Sarakunan dai sun haɗa da Manjo Muhammad Iliyasu Bashar Sarkin Gwandu (murabus), Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera CON, Sarkin Yawuri Alhaji Muhammad Zayyanu Abdullahi da kuma Sarkin Zuru Janar Muhammad Sani Sami (murabus).

PDP ta gargaɗi Gwamna Nasir:

Jam’iyyar PDP  reshen jihar Kebbi ta shiga sahun taya dukkan al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai. 

Sai dai ba nan gizo ke saƙa ba, don kuwa a jihar Kebbi Jam’iyyar PDP ta adawa a cikin saƙonta na taya ɗaukacin ‘yan Nijeriya murnar ta koka bisa ga yadda ta ce gwamnan jihar Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu yana yi wa kuɗin jihar kisan macijin mata.

Takardar da jam’iyyar PDP ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na jiha Honarabul Abubakar Bawa Kalgo (ABK), Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi zuwa ga Gwamnan jihar  bisa girmamawa cewa a daina yi wa kuɗi kisan macijin mata, kuma a taƙaita kisan kuɗi ta hanyar gudanar da mulki ta hanyoyin da kisan kuɗin ba ya da amfani ga ‘yan jihar sai  dai wajen  muƙarraban gwamnan.

Takardar ta yi kira ga Gwamnan da sauran muƙarrabansa da su ji tsoron Allah a cikin sha’anin gudanar da mulkinsu, kuma su yi adalci su tarairayi dukiyar al’umma a bisa ga amanar da Allah ya ba su. 

Haka-zalika, ta ja hankalin gwaman da ya yi ƙoƙari ya yi amfani da damar da ya samu ya yi koyi da magabata na ƙwarai da suka bar tarihi mai kyau wanda a dalilin haka ne sunansu ba zai ɓata ba har abada, saboda sun yi adalci sun aiwatar da ayyuka da suka taɓo zuciyar talakawa da suka ƙunshi fannonin lafiya da aikin gona da ilmi da da dai sauran ɓangarorin rayuwa tun kama daga birane zuwa ƙauyuka.

Takardar ta ja hankalin gwaman musamman da ya ke shi malamin makaranta ne kuma ya yi shige da fice wajen neman haƙƙoƙan malamai.

“To idan da gaske ne ba yaudara a ciki ya kamata ya waiwayo ɓangaren malamai musamman na firamare saboda yana daga cikinsu kuma ya san irin alƙawarin da ya musu a baya lokacin yaƙin neman zaɓe.

Daga ƙarshe takardar ta yi addu’ar Allah ya kawo sauƙin rayuwa a wannan ƙasar tare da zaman lafiya mai ɗorewa.

By ukarofi