Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe kujeru 22 daga cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka kammala a Jihar Ribas.
Babban Jami’in Zabe na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas, Mai Shari’a Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon zaɓen ranar Asabar a Fatakwal.
Ya ce an dakatar da sanarwar ne a karamar hukumar Etche saboda har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.
Sauran bayanai na zuwa…
