’Yan Maulidi 150 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Neja

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani lamari mai ban takaici, sama da fasinjoji 150 ne ake fargabar sun mutu bayan da wani kwale-kwale ɗauke da mutane sama da 300 ya kife a jihar Neja.

Kwale-kwalen ya cika maƙil da yawancin mata da ƙananan yara, yana kan hanyarsa ta zuwa al’ummar Gbajibo daga Mundi domin gudanar da bikin Maulidi a lokacin da ya nutse a cikin ruwan kogin Neja da yammacin ranar 1 ga Oktoba, 2024.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, kwale-kwalen da ya yi mugun lodi, ya yi ta ƙoƙarin ci gaba da tafiya kafin ya kife. Fasinjojin dai na gudanar da wani tafiyar addini ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Lamarin ya faru ne a kusa da yankin Gbajibo, ɗaura da madatsar ruwan Jebba, kuma ya jefa yankin cikin ɗimuwa. Nan take aka ƙaddamar da aikin ceto, inda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta haɗa kai da ma’aikatar sufuri ta jihar, da kwamitin gaggawa na ƙaramar hukumar Mokwa, da masu ruwa da tsaki, da masu aikin sa kai na al’umma. Duk da saurin mayar da martanin da suka bayar, amma mutane kaɗan nw aka samu damar cetowa.

Alhaji Abdullahi Baba-Arah, Darakta Janar na Hukumar NSEMA, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce: “NSEMA ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a daren ranar 1 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare a gabar kogin Neja, ɗaura da madatsar ruwan Jebba, a unguwar Gbajibo da ke ƙaramar Hukumar Mokwa.”

Tawagar masu aikin ceto na ci gaba da ƙoƙarin gano gawarwaki tare da neman waɗanda suka tsira da rayukansu, duk da cewa magudanar ruwan kogin na da sarƙaƙiya.

By ukarofi