Na yi wa Tinubu yaƙin neman zaɓe, don haka na yarda da hukuncinsa kan garambawul – Ministar Al’adu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta ce ba ta damu da shirin garambawul na ministoci da Majalisar Zartarwa (FEC) ke yi ba ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministar ta faɗi hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na ‘channels’ inda ta ce ta san ta yi wa Tinubu yaƙin neman zaɓe kuma ta yarda da hukuncinsa.

Ta ce, ta san shugaban ƙasar ya na da manufa da burin sauya Nijeriya daga halin da take zuwa yanayi mai kyau, ta na mai cewa hakan ba zai samu ba ba tare da mataimaka masu jajircewa ba.

Ta ƙara da cewa, kasancewar ana buƙatar samar da sakamako masu kyau a kowane ɓangare ƙarƙashin kyawawan manufofin Shugaba Tinubu, rashin samun jajircewa daga ministoci, illa ce ga ƙoƙarin cimma hakan.

A baya ne aka samu kiraye-kiraye ga Shugaba Tinubu kan ya tsige wasu daga cikin ministocin nasa da ba sa aiki yadda ya kamata wanda a watan Satumba ne Kakakinsa, Bayo Onanuga ya ce shugaban ya nuna muradin yin garambawul wa ministocinsa amma bai faɗi lokacin da za a yi hakan ba.

By Babaji